An bukaci Jam’iyyar APC ta hana Godwin Obaseki tsayawa takara a Edo
Tirka-tirka game da wanda zai rikewa jam’iyyar APC tuta a zaben gwamnan jihar Edo a Satumba mai zuwa ya na kara karfi inda ake neman haramtawa gwamna Godwin Obaseki takara.
Rahoton da mu ka samu daga jaridar This Day ya bayyana cewa an taso APC a gaba ta hana gwamna mai-ci Godwin Obaseki samun damar sake tsayawa takarar da za a yi a jihar Edo.
Ana so shugabannin jam’iyyar su hana Obaseki tsayawa takara ne saboda haka-da-haka da aka samu a game da takardun shaidarsa, wanda hakan na iya jawowa APC matsala a zaben.
Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su na tsoron kotu ta yi masu irin abin da ya faru a jihar Bayelsa, inda takardun shaida su ka hana a rantsar da David Lyon ana gobe zai hau mulki.
Masu wannan kira sun tunawa APC yadda matsalar bambance-bambancen suna a satifiket su ka jawo APC ta gaza karbe mulki a Bayelsa duk da cewa ta lashe zaben gwamnan da aka yi.
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa
Daga cikin matsalar da ake samu da Godwin Obaseki shi ne bai samu nasara a jarrabawar O’Level ta kammala sakandare ba, amma kuma duk da haka ya samu shiga jami’ar Ibadan a 1974.
Bayan haka Obaseki ya kammala Digiri ne a jami’ar cikin shekara uku, duk da bai yi karatun sharan fage na A’Level ba. A doka ba a yin shekara uku a jami’a daga karkare sakandare.
Zargin yadda Obaseki ya samu tafiya jami’a bayan kwas uku kurum ya ci a jarrabawar O’Level zai zama abin tambaya nan gaba a kotu. Haka kuma yadda ya kammala Digiri a shekara uku.
Akwai kuma irin wannan matsala a takardun Chris Ogiemwonyi, wanda shi ma ya na neman tikitin gwamna a APC. Ogiemwonyi ya na ikirarin yayi karatu ne dai a jami’ar ta Ibadan.
Yanzu haka wannan korafi ya kai gaban kwamitin da ke tantance ‘yan takarar APC a zaben. Wadanda su ka kai kukan su ne Edobor Williams, Ugbesia Godwin da Amedu Anakhu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng