Majalisar Dattawa ta na hasashen za a saida gangar man fetur a kan $28

Majalisar Dattawa ta na hasashen za a saida gangar man fetur a kan $28

- Sanatoci sun maida lissafin kudin gangar mai $28 a kasafin shekarar 2020

- An kara kudin da ake sa ran samu ne saboda yadda kasuwa ke tafiya a yau

Majalisar dattawan tarayya ta yi gyara game da hasashen da gwamnatin tarayya ta yi kan kudin da ake sa ran za a samu daga man fetur a kasafin kudin shekarar nan mai-ci.

Bayan zaman farkon da aka yi a makon nan, sanatocin Najeriya sun maida lissafin kowace gangar mai kan Dala $28. Gwamnatin tarayya ta tsaida lissafin ta kan Dala $25.

An ci ma wannan matsaya ne a ranar Talata, 2 ga watan Yuni 2020 bayan shugaban kwamitin tattalin arziki, sanata Solomon Olamilekan ya gabatar da rahotonsa a majalisar.

Ganin halin da ake ciki a yanzu na tabarbarewar tattalin Duniya, majalisar ta bada shawarar tsaida farashin Dala a kan N360, sannan a guji karya darajar Naira a nan gaba.

Har ila yau, majalisar ta tsaida danyen man da za a hako duk rana a kan ganguna miliyan 1.8.

KU KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya zai murmure bayan danyen mai ya kara kudi

Sanata Solomon Olamilekan ya kuma yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara kokari wajen fadada hanyar samu da karfin tattalin arzikin Najeriya.

An yi wadannan gyare-gyare ne a tsarin MTEF da FSP sakamakon karyewar farashin mai a Duniya a dalilin annobar cutar Coronavirus da ta shafi Najeriya da sauran kasashe.

‘Yan majalisar tarayyar sun yi kira na musamman ga hukumar mai na kasa nta NNPC da ta rage adadin danyen man da ta ke hakowa, hakan ya zo daidai da yarjejeniyar OPEC.

An kuma bukaci gwamnatin tarayya ta dage wajen samun kudin shiga ta hanyoyin haraji. Wannan kwamiti na majalisar dattawan ya yi magana kan toshe kafar facaka.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya amince da duk shawarwarin da kwamitin ya kawo. Ya ce an kara kudin da aka yanke ne saboda ganin yadda mai ya fara tashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel