Gangan danyen man ‘Brent’ ya haura $40 a kasuwar Duniya

Gangan danyen man ‘Brent’ ya haura $40 a kasuwar Duniya

- Gangar danyen mai ya na kara kudi a kasuwannin kasahen Duniya

- Farashin gangar Brent ya haura $40 a karon farko tun watan Maris

- Man ya kara daraja bayan OPEC ta rage yawan abin da ta ke hakowa

Farashin gangar danyen mai ya na tashi a kasuwar kasashen Duniya.

Babu shakka wannnan labari ne mai dadi ga kasashe irinsu Najeriya da su ka dogara da arzikin mai.

A cikin farkon makon nan gangar danyen man Brent ya kai har Dala $40.42 a kasuwar Duniya. Mai bai taba yin irin wannan tsada a kasuwa ba tun cikin farkon Maris.

A ranar Talata 2 ga watan Yuni, 2020, farashin wannan samfari na mai ya kara kudi da fiye da kashi 3.3%, kamar yadda mu ka samu rahotanni daga jaridun kasashen waje.

A daidai wannan lokaci gangar man WTI na kasar Amurka ya kara farashi da kusan 2.0%. Man WTI wanda ake saida gangarsa a kan $37.49 ya tashi zuwa $37.88 a makon nan.

KU KARANTA: Ya kamata litar fetur ya zama N70 - PDP

A ranar Talatar ne kuma majalisar tarayyar Najeriya ta taba lissafin da aka yi na abin da ake hasashen kasar za ta samu, hakan bai rasa nasaba da yadda kasuwar ta ke tafiya.

Sanatoci sun yi hasashen cewa za a saida gangar man Najeriya a kan $28 a kasuwar Duniya, akasin fam Dala $25 da shugaba Muhammadu Buhari ya yi lissafi a kwanakin baya.

Kungiyar OPEC ta kasashen da ke fitar da mai a Duniya ta na tunanin cigaba da rage adadin danyen man da ta ke hakowa har zuwa cikin watannin Yuli da Agusta da za a shiga.

Rasha da sauran kasashen OPEC ba su hako abin da ya haura ganga miliyan 9.7 duk rana. Wannan ya na nufin an rage kusan 10% na abin da ake samu a kasuwannin mai.

A cikin watan Afrilu sai da farashin gangan man Brent ya karye zuwa $15. Tun daga lokacin da OPEC ta rage adadin abin da ake hakowa, danyen man ya rika kara daraja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel