AGF: Shari’ar Hamisu Wadume ta koma karkashin ofishin Ministan shari’a

AGF: Shari’ar Hamisu Wadume ta koma karkashin ofishin Ministan shari’a

Ofishin ministan shari’ar Najeriya kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ta karbe shari’ar da ake ta faman yi da Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume a jihar Taraba.

Idan ba ku manta ba jami’an tsaro su na tuhumar Hamisu Bala ‘Wadume’ da wasu laifuffuka 16 wanda su ka hada har da garkuwa da mutane da ta’addanci da kuma kisan kai.

Tun a watan Fubrairu ne shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa ya kai karar Wadume a gaban kotu. Ana karar Wadume ne tare da wani jami’in soja mai suna Tijjani Balarabe.

‘Yan sanda su na zargin Kyaftin Tijjani Balarabe ya na da hannu a wani yunkuri da aka yi na tserewa da Wadume, wanda har hakan ya jawo aka kashe wasu ‘yan sanda biyu.

A yayin da ake wannan shari’a yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020, sai wani babban jami’in ma’aikatar shari’a, Shuaibu Labaran, ya fadawa kotu karar ta koma hannun AGF

KU KARANTA: IGP ya gaza gurfanar da Wadume a kotu bayan dogon lokaci

AGF: Shari’ar Hamisu Wadume ta koma karkashin ofishin Ministan shari’a
Hamisu Wadume Bala Hoto: NPF
Asali: UGC

Labaran ya roki Alkali ya kara lokaci domin ofishin ministan ya samu damar karantar shari’ar, wanda hakan zai taimakawa ministan daukar matakin da ya dace a gaban kuliya.

AGF ya dawo da shari’ar wannan tuhuma a karkashin hannunsa. Mun karbi takardun, kuma mun lura cewa akwai mutane kusan 20 da ake zargi da laifin” inji mista Labaran.

Ya ce: “Saboda haka akwai bukatar mu karanci shari’ar, sannan kuma mu hada-kai da jami’an tsaro domin ganin cewa an gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kotu.”

Ma’aikatar shari’ar za ta nemi ta zauna da jami’an da su ka kama wadanda ake zargi. A karshe Labaran ya ce: ”Za mu yi bakin kokarinmu na ganin an yi adalci a wannan kara.”

Alkali mai shari’a Binta Nyako wanda ta ke sauraron karar ta dakatar da zama sai ranar 8 ga watan nan. Ana sa ran a wannan rana ne za a sake gurfanar da wadanda ake zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel