Motoci uku muka siyar kafin karbo mahaifinmu - Dan shugaban CAN ya bayyana

Motoci uku muka siyar kafin karbo mahaifinmu - Dan shugaban CAN ya bayyana

Miracle, dan Joseph Masin, shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Nasarawa, ya ce iyalansa sun siyar da motoci uku kafin biyan kudin fansa don sakin mahaifinsu.

An yi garkuwa da Masin a ranar 28 ga watan Mayu yayin da 'yan bindiga suka kutsa gidansa wurin karfe 11 zuwa 12 na dare. Bayan kwanaki uku kuwa sai masu garkuwa da mutanen suka sako shi.

A wata tattaunawar da jaridar The Punch ta yi da Miracle, ya ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 50. Sun siyar da motoci uku don samun kudin fansar.

"Mun biya miliyoyin naira amma bamu shirya sanar da ko nawa muka kashe ba. Mun matukar takura amma muna godiya ga Ubangiji.

"Mun fara ciniki tun ranar da aka yi garkuwa da shi har zuwa ranar da aka sako shi, Asabar 30 ga watan Mayu wurin karfe 11:45 na dare. Ya iso gida wurin karfe 4 na asuba," yace.

Motoci uku muka siyar kafin karbo mahaifinmu - Dan shugaban CAN ya bayyana
Motoci uku muka siyar kafin karbo mahaifinmu - Dan shugaban CAN ya bayyana Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Mahaifina bai san inda yake ba har sai da ya hadu da wasu jama'a. Suna gudunsa saboda halin da suka gan shi a ciki amma daya daga cikinsu ne ya samu karfin guiwar tambayarsa. Daga baya ne suka taimaka masa.

"A cikin kwanakin, mahaifinsa baya iya cin abinci. Suna bashi abinci, amma baya iya ci saboda bai yarda da su ba.

"Sun sako shi a kusa da Eggon amma an biya kudin fansar a Obi ne."

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Ana rikita-rikita a kan shugabancin kotun daukaka kara

Miracle ya kara da cewa gwamnatin jihar bata bada ko sisin kwabo ba wajen biyan kudin fansar mahaifinsa.

A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ba zai kara yin sulhu da 'yan bindiga ba saboda cin amanar da aka yi wa gwamnatinsa.

A cewar gwamnan, barayin da ke fashi a dazuka sun ci amanar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da su.

Yayin hirarsa da sashen Hausa na BBC, Masari ya ce wasu daga cikin 'yan bindigar da ke kai hare - hare a jihar Katsina akwai wadanda su ka fito daga jihar Kaduna da Zamfara da 'yan Nijar.

Masari ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta fara zuwa da tsarin yin sulhu da 'yan bindiga a shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel