Haramta Almajiranci ba zai kawo karshen barace-barace ba Inji Rochas Okorocha
Jaridar BBC Hausa ta yi hira da tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha inda ya nuna rashin goyon bayansa game da shirin da wasu gwamnoni ke yi na hana almajiranci.
Sanata Rochas Okorocha ya dauko tarihin almajiranci wanda ya ce kalmar ta samo asali ne tun daga mutanen da su ka yi hijira, su ka tare wajen Annabi Muhammad SAW a garin Madina.
Rochas Okorocha ya gargadi gwamnonin Arewa cewa maida Almajirai jihohin da su ka fito ba zai sa su daina bara ba, a cewarsa yin hakan kawai ba zai sa su iya daukar dawainiyar kansu ba.
Okorocha ya bada shawarar a hada-kai, a rika taimakawa wadannan Bayin Allah da su ke fama da yunwa da talauci domin su samu ilmi, su kuma koyi sana’ar da za ta rike su kamar noma.
Sanatan mai-ci ya ke cewa mafi yawan manyan mutanen da ake da su yanzu, sun yi almajiranci a baya. Wannan ya sa tsohon gwamnan ya ke ganin ya fi kyau a inganta wannan tsarin ilmin.
KU KARANTA: Sheikh Gumi ya fadi dalilan da su ka sa Gwamnati ta bude Masallatai
“Na san zafin da gwamnoni su ke ji, a yanzu mutane su na bukatar ayi masu hanyoyi, a biya ma’aikata, cikin kudin da su ke da shi, akwai wahala. Amma a taimaki ‘dan talaka tukuna.”
“Idan an taimake su, sai kuma a nemi hanyar da za ayi wasu abubuwa. Idan aka ba su wajen kwanciya ko aka koya masu sana’ar hannu, za su iya ciyar da kansu.” Inji Rochas Okorocha.
“Idan ba ayi wani abu game da lamarin talauci musamman a Arewa ba, tabbas za a samu matsala nan gaba. Yaran nan fa ba laifinsu ba ne, Allah ne ya hallicesu, su ka tashi a inda babu hali.”
Fitaccen ‘dan siyasar ya yarda bara ya sabawa koyarwar musulunci, amma ya ce dole ce ta sa su ka koma bara wajen karatu don haka ya ce nauyi ne a kan shugabanni su kawo masu mafita.
A hirar, Okorocha ya shaidawa jaridar yadda makarantun da gidauniyarsa ta gina ta ke kokarin ba yara manyan gobe ilmi a irinsu Garuruwan Sokoto, Zariya, Kano, Bauchi, Jos, Yola da Kano.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng