Yanzu-yanzu: Oshiomhole ya bayyana irin zaben fidda gwanin da za a yi a Edo

Yanzu-yanzu: Oshiomhole ya bayyana irin zaben fidda gwanin da za a yi a Edo

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya jaddada cewa sai dai a yi zaben kato bayan kato yayin zaben fidda gwani na gwamnan jam'iyyar APC a jihar Edo.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta bada ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar yin zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Edo.

Ya bayyana wannan hukuncin ne bayan taron da yayi da kwamitin ayyuka da kuma gwamnonin jam'iyyar APC na jihohin fadin kasar nan.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ne bayan taron da ya dauka tsawon sa'o'i uku w sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a kokarin ceto Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun tsinkayi ofishin jam'iyyar a ranar Litinin don yin taron toshe baraka da Kwamared Adams Oshiomhole.

An sake shiga wani taron makamancin hakan da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu a garin Legas.

KU KARANTA KUMA: Sokoto: FG ta yi kira ga cibiyoyi da su mika tallafi ga wadanda harin 'yan bindiga ya shafa

A halin yanzu ana ci gaba da taron a dakin taro da ke ofishin jam'iyyar da ke Abuja tare da shugaban jam'iyyar na kasa wanda ke jagoranci.

Gwamnonin da suka samu halartar taron sun had a da Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredoku, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa.

Sauran sune Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaki.

Har ila yau, Gwamna Godwin Obaseki ya gaggauta kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari fadarsa da ke Aso Villa a Abuja.

Ya kai ziyarar ne sakamakon zaben fidda gwani da ke tunkaro jiharsa da kuma rikicin da ke tsakaninsa da Kwamared Adams Oshiomhole a jihar Edo.

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

An tattaro cewa Obaseki ya shiga damuwa bayan ya fahimci cewar Oshiomhole na shirya ma sa tuggun da zai iya jawo ma sa rasa kujerarsa a zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Edo wanda za a yi a cikin watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng