Rikicin jam'iyyar APC: Tsohon kakakin majalisa ya aika wa Buhari muhimmin sako

Rikicin jam'iyyar APC: Tsohon kakakin majalisa ya aika wa Buhari muhimmin sako

Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Edo, Alhaji Kabiru Adjoto, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka ya shiga cikin rudanin da jam'iyyar ke ciki a jihar.

Adjoto, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar jihar, ya yi wannan kira ne a ranar Litinin a Benin yayin da yake karbar bakuncin shugabannin jam'iyyar daga yankin Edo ta arewa.

Jigon na jam'iyyar APC din ya ce idan shugaban kasar ya shiga al'amarin, akwai yuwuwar samun gagarumar nasara a zaben gwamnoni da ke tunkarowa a watan Satumba mai zuwa.

Adjoto ya kara da cewa rikicin jam'iyyar na ci gaba da kamari a jihar.

Rikicin jam'iyyar APC: Tsohon kakakin majalisa ya aika wa Buhari muhimmin sako
Rikicin jam'iyyar APC: Tsohon kakakin majalisa ya aika wa Buhari muhimmin sako Hoto: The Cable
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saka ranar 22 ga watan Yuni, a matsayin ranar zaben fidda gwani na gwamnoni a jihar yayin da 19 ga watan Satumba za ta zama ranar zaben gwamnonin.

Wannan ci gaban ya sake assasa ruguntsumin rigima tsakanin sassa biyu na jam'iyyar APC a jihar.

Adjoto ya ce, "Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya bai wa jam'iyyar damar zaben yadda zaben fidda gwanin zai kasance.

"Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Edo sun amince da yin zaben fidda gwani wanda ba na kai tsaye ba saboda annobar Coronavirus da kuma rashin rijistar mambobi," yace.

Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da su tattauna da Adams Oshiomhole don gujewa faduwar jam'iyyar a zaben da za a yi a watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Sabon kasafin kudi: Tashin hankali da tarzoma ta barke a majalisar tarayya

A gefe guda Legit.ng ta rahoto a baya cewa rikicin jam'iyyar APC ya sauya wani salo mai karfin gaske, yayin da gwamnoni tara suka gana da Asiwaju Bola Tinubu, dangane da zaben gwamna da ke tafe a jihohin Edo da Ondo.

Gwamnonin karkashin kungiyar ci gaban gwamnoni ta PGF, wanda gwamnan jihar Kebbi ya jagoranta, sun gana ne a gidan gwamnatinsa da ke unguwar Marina a jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel