Sokoto: Yadda rayuka 270 suka salwanta a cikin hari 20

Sokoto: Yadda rayuka 270 suka salwanta a cikin hari 20

Sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai garin Sokoto wanda yayi ajalin rayuka 70, wata kungiyar 'yan jihar Sokoto ta yi kiran gaggawa ga gwamnati a kan ta dauki mataki da wuri.

Kungiyar ta bayyana cewa, daga watan Janairun da ya gabata, an rasa a kalla rayuka 270 a jihar sakamakon hare-hare 20 da 'yan bindiga suka kai jihar.

A yayin jawabi ga manema labarai a madadin kungiyar, Farfesa Nasiru Gatawa ya ce suna cikin matsanancin hali don haka suna bukatar gwamnati ta dauka matakan gaggawa.

Kamar yadda yace, "muna da kananan hukumomi 8 a yankin gabashin jihar. Sun hada da: Gada, Goronyo, Gwadabawa, Illeila, Issa, Rabbah, Sabon Birni da Wurno.

"Yankin da aka fi takura wa shine Sabin Birni. 'Yan bindigar na kai kawo yadda suke so da rana tsaka ba tare da wani yunkurin hana su ba daga gwamnati.

"Kowacce daga cikin kanana hukumomin na karkashin 'yan ta'adda don sun gurgunta tattalin arzikinsu tare da asarantar da rayuka da kadarori," yace.

Sokoto: Yadda rayuka 270 suka salwanta a cikin hari 20
Sokoto: Yadda rayuka 270 suka salwanta a cikin hari 20 Hoto: Channels Television
Asali: UGC

A yayin jajanta harin da aka kai a ranar Laraba, Farfesan ya ce, "kowacce daga cikin gunduma 11 ta karamar hukumar Sabon Birni na karkashin 'yan bindiga kuma sai da yardarsu ake bikin aure, suna idan an haihu da kuma cin kasuwa.

"A yanzu da muke magana, hatta sauran kananan hukumomi 8 na yankin gabashin jihar Sokoto na cikin firgici.

"Al'amarin kullum karuwa yake don hatta garin Sokoto basu tsira daga harin 'yan bindigar ba da ke kusantowa zuwa garin," yace.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Za a fara tura wa jama'a tallafin kudi don rage radadi a Legas

Farfesa Gatawa ya kara da tunatar wa a kan yammacin ranar Idi da 'yan bindigar suka kai hari kauyen Ummaruma inda suka kashe wani hamshakin dan kasuwa.

A kwanaki kadan da suka gabata ne sanatan da ke wakiltar yankin Sokoto na gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gobir, ya yi ikirarin cewa a wani bangare na mazabarsa, 'yan bindiga ne ke sasanta mata da miji idan an samu tashin hankali.

Ya zargi 'yan bindigar da kafa alkalansu tare da tsige sarakunan gargajiya a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng