Zaben kananan hukumomi ya wargaza Jam’iyyar APC a jihar Kuros-Riba
- Jam’iyyar APC ta na fama da matsala a Jihar Kuros Riba tun ba yau ba
- Zabukan kananan hukumomi sun karfafa barakar cikin gidan Jam’iyyar
- Wasu ‘Yan APC sun janye jiki daga takarar, wasu bangare sun ce atafau
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa bangarorin jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba sun sake barkewa da rigimar cikin gida. Zaben da za ayi kwanan nan ne ya sake tado da rikicin.
A karshen makon nan ne ake sa ran za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a fadin jihar Kuros-Riba. Wani bangare na jam’iyyar APC sun ce ba za su shiga wannan takarar ba.
A daidai wannan lokaci kuma, wani bangare sun fito sun nuna cewa za a yi wannan zabe da su. Mutanen Godwin Etim John su ne su ke ikirarin za a fafata da ‘yan takararsu na APC.
Shi kuma Sir John Ochala wanda ya ke da’awar shi ne ainihin shugaban APC na Kuros Riba ya ce ‘yan takarar jam’iyyar adawar ba za su shiga zaben ba saboda sabawa dokoki da aka yi.
KU KARANTA: Hedikwatar hukumar Neja-Delta ta tashi aiki saboda rasuwar Darekta
A wani jawabi da Godwin John ya fitar ga manema labarai, ya zargi bangaren John Ochala da zama sojojin hayar wasu jam’iyyun, ya kuma soki matakin da su ka dauka na janye jiki.
“Mu na so mu yi wa jama’a karin-haske, APC ba za ta kauracewa zaben kananan hukumomin da za a yi a karshen mako ba. Mu na da ‘yan takararmu a shirye.” A cewar Godwin John.
Shi kuma Ochala da majalisarsa sun ruga kotu, inda su ke tuhumar hukumar zabe na jihar, CROSIEC, don haka su ka nemi dakatar da gudanar da wannan zaben kananan hukumomin.
Har zuwa yanzu bangarorin na APC masu hamayya a Kuros Riba ba su iya cin ma maslaha ba. Haka zalika uwar jam’iyyar ba ta sa baki a rikicin da ya dade ya na raba kan APC a jihar ba.
A daidai wannan lokaci, shugaban hukumar CROSIEC, Mike Ushie ya fito ya ce APC ta na da ‘yan takara a zaben, duk da rahotannin da ke yawo na cewa jam’iyyar ba za ta yi takara ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng