Fashi da makamai: Alkali ya yanke hukuncin kisa ta rataya a jihar Osun

Fashi da makamai: Alkali ya yanke hukuncin kisa ta rataya a jihar Osun

- Kotu ta samu wasu mutane biyu da laifin fashi da makami a Jihar Osun

- Alkali ya yankewa wadannan miyagun hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Wadannan mutane sun aikata laifin fashi da makami ne a shekarar 2016

A ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2020 wata babbar kotu a jihar Osun ta yankewa wasu mutane biyu da aka samu da aikata laifin fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkali mai shari’a, Jide Falola, ya ce a rataye wadannan miyagun mutane biyu har sai sun mutu. Alkalin ya yanke wannan mummunan hukunci ne saboda girman laifin da aka aikata.

An zargi wadannan miyagu da laifuffuka biyar wadanda su ka hada da fashi da makami, sata da kutun-kutun din aikata laifi. A karshe kotu ta kuma same su da laifin da aka ambata.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa an tabbatar da wannan hukunci ne a gidan kasonIlesa a wata ziyara da alkalin alkalan jihar Osun, Adeleke Ojo, ya kai kurkukun.

KU KARANTA: Kotu ta raba gardamar da ke tsakanin INEC da Jam'iyyun siyasa

Alkali Jide Falola ya samu ‘yan fashin da laifi a lokacin da ya saurari shari’arsu. Lauyan gwamnati ya shaidawa kotu cewa wadannan mutane sun aikata laifin ne a Afrilun 2016.

Muyiwa Ogunleye wanda ya tsayawa hukuma ya ce wanda ake zargin sun hada-kai da wasu, sun sacewa wani Muideen Owonifari, Clement Taiwo da Olubunmi kudi da kayan arziki.

Ogunleye ya ce: “Sun yi fashi, sun kuma ci mutunci, sannan sun saci wasu dukiyoyi da makudan kudi na wadanda su ka kawo kuka.” An yi fashin ne a yankin Oke-Ola, jihar Osun.

Laifin fashi da makami ya sabawa dokokin kasa wanda su ka haramta rike makamai da satar abin hannun wani. Wannan ya sa lauyan wadanda ake tuhuma ya nemi rangwame.

Alkali bai saurari rokon lauyan da ya tsayawa ‘yan fashin ba watau L.S Bello, inda ya yanke masu hukunci mafi tsauri. Yanzu ana jiran sa-hannun gwamnati, a rataye marasa gaskiyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel