Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shugaban CAN

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shugaban CAN

- Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kungiyar kiristoci na jihar Nasarawa (CAN), Bishop Joseph Masin

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe ne ya tabbatar da aukuwar lamarin

- Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi gaba da shugaban CAN din ne a kan babura

An yi garkuwa da shugaban kungiyar kiristoci na jihar Nasarawa (CAN), Bishop Joseph Masin.

Tsohon sakataren kungiyar kiristocin ta kasa, Yohanna Samari ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a garin Lafia.

Ya ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka tsinkayi gidan shugaban kungiyar a cikin dare. Gidansa na yankin Bukan Sidi da ke garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shugaban CAN
Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shugaban CAN Hoto: The Cable
Asali: UGC

Tuni suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe ne ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi gaba da shugaban CAN din ne a kan babura.

Longe ya kara da cewa jami'an 'yan sanda na kokarin bankado inda masu garkuwa da mutanen suke don ceto rayuwan shugaban ba tare da wani hatsari ba.

KU KARANTA KUMA: Tsaro: N7bn ce masu garkuwa da mutane suka karba cikin shekaru 9 a Najeriya

A gefe guda mun ji cewa jami’an hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.

Punch ta ruwaito baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansan da iyayensa suka biya don a sake shi.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu aka yi garkuwa da yaron a gidan Shehin dake jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.

Muhammad Alhassan ya bayyana cewa sun samu nasarar kama mutumin ne tare da hadin gwiwar hukumar Yansandan jahar Kano.

Daga karshe Alhassan yace za su mika mutumin ga Yansanda don su gurfanar da shi gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel