Siyasa: Shugabannin PDP sun samu sabani a Filato, Ekiti, Kaduna da Ogun
- Jam’iyyar PDP ta samu kan ta a cikin sabanin shugabanci a wasu Jihohi
- Jihar Kaduna, Ekiti da Filato su na cikin inda wannan rigima ta yi kamari
- Lamarin ya kai an samu ‘yan taware ko kuma an kori wasu ‘yan jam’iyya
Jam’iyyar hamayya ta PDP ta shiga tsilla-tsilla a jihohin Filato, Ekiti, Kaduna, Ogun saboda lissafin siyasar 2023 kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust.
Jaridar ta ce ana samun sabani a babbar jam’iyyar adawar kasar ne a dalilin kokarin da jiga-jigan ‘yan siyasa su ke yi na ganin jam’iyya ta na karkashinsu kafin zabe mai zuwa.
Wasu jagororin jam’iyyar su na ganin idan uwar jam’iyya a karkashin Prince Uche Secondus ba ta yi maza ta sa baki ba, abubuwa za su kai ga cabewa PDP a babban zaben 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa a jihar Filato, PDP ta barke gida biyu inda tsakanin Hon. Nandom Pyennap da Yakubu Choco, kowane ya ke ikirarin shi ne shugaban PDP a jihar.
KU KARANTA: Yadda PDP za ta fito da 'Dan takararta a zaben 2023 - Sule Lamido
Bangaren Pyennap su na da goyon bayan ‘dan takarar gwamnan jam’iyyar a zaben 2019, Jeremiah Useni. Yayin da Choco ke tare da tsohon gwamna Jonah Jang da wasu manyan PDP.
A Ekiti rigimar har ta kai an gudanar da mabanbantan zaben shugabanni. Kawo yanzu akwai kara a kotu inda aka bukaci ayi watsi da zaben da Haruna-Manu ya shirya kwanaki.
A zaben 2019, jihar Kaduna ce ta ba jam’iyyar PDP mafi yawan kuri’un da ta samu a zaben shugaban kasa. A Kaduna rigimar cikin-gidan har ta sa an kori wasu kusoshin PDP.
Sanata Suleiman Hunkuyi da Dr. John Danfulani da wasu mutane hudu su na cikin wadanda aka dakatar ko kuma har ta kai an kore su daga jam’iyyar bisa zargin shirya zagon-kasa.
Danfulani da Ubale Salmanduna wadanda su na cikin wadanda kwamitin Hamza Danmahawayi ya bukaci a kora daga PDP, sun fito sun ce shugabannin jihar ba su da ikon korarsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng