Jigawa: Almajirai 122 sun kamu da kwayar cutar COVID-19 inji Badaru

Jigawa: Almajirai 122 sun kamu da kwayar cutar COVID-19 inji Badaru

- Almajirai 122 aka samu su na da cutar COVID-19 a Jihar Jigawa

- Gwamna Muhammad Badaru ya bayyanawa Duniya wannan jiya

- Hakan na nufin rabin masu cutar COVID-19 a jihar, Almajirai ne

A ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2020, mai girma gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya bayyana cewa an samu wasu Almajirai rututu da ke dauke da cutar COVID-19.

Gwamna Muhammad Badaru ya ce Almajirai da ke yawon bara a titi har 122 aka samu da kwayar cutar COVID-19. An tabbatar da wannan ne bayan an yi masu gwajin wannan cuta.

Badaru ya shaidawa ‘yan jarida wannan a wani taron zantawa da manema labarai da ya shirya a babban birnin Dutse. Gwamnan ya ke cewa an dawo masu da Almajirai fiye da 1, 300.

Almajirai 1, 345 wadanda ainihin ‘yan jihar ne sun komo gida sakamakon annobar COVID-19.

An dawo da Almajiran ne daga Nasarawa, Kano, Kaduna, Filato, Adamawa da Gombe.

KU KARANTA: Aikin Dangote ya tsaya yayin da Coronavirus ta kama mutum 900 a Kano

Jigawa: Almajirai 122 sun kamu da kwayar cutar COVID-19 inji Badaru
Gwamna Muhammad Badaru Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

“An killacesu a sansanin NYSC. An yi wa dukkansu gwajin kwayar COVID-19. A karshen zamansu, sakamakon gwaji ya nuna 122 daga cikinsu su na da cutar.” Inji Badaru.

Gwamnan ya kuma shaida cewa 51% na masu dauke da cutar Coronavirus yanzu a Jihar Jigawa, Almajirai ne. Sauran Almajiran da ba su kamu da cutar ba, duk sun koma gidajensu.

Kafin a saki Almajiran, gwamnatin Jigawa ta ba su tufafi da alawus na N10, 000. Bugu-da-kari, za a zuba ‘yan makarantar allon da tsangaya cikin makarantun boko a cewar gwamnan.

Bayan haka, gwamna Badaru ya ce jihar Jigawa ta kafa dakin yin gwajin COVID-19 da sauran cututtuka. Wannan ya na cikin kokarin da gwamnatimsa ta ke yi na yaki da annobar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel