Kiyayya da keta: An kori 'yan sandan kasar Amurka 4 da su ka kashe wani bakar fata (bidiyo)

Kiyayya da keta: An kori 'yan sandan kasar Amurka 4 da su ka kashe wani bakar fata (bidiyo)

An kori 'yan sanda hudu a jihar Minneapolis ta kasar Amurka bayan faifan bidiyonsu su na cin zalin wani bakar fata ya watsu a yanar gizo, musamman a dandalin tuwita.

An kori 'yan sandan ne ranar Talata bayan an fara zanga - zanga a birnin Minneapolis domin nuna bacin rai a kan kiyayyar da fararen 'yan sandan su ka nuna a kan bakar fata mai suna George Floyd.

A cikin faifan bidiyon, an ga daya daga cikin 'yan sandan ya dira gwuiwarsa a wuyan Floyd yayin da hannunsa ke daure da ankwa ta baya.

Duk da ihun da Floyd ke yi na cewar ba ya iya numfashi saboda dan sandan ya danne ma sa wuya, hakan bai sa sauran 'yan sandan sun kwace shi ko sun tsawatarwa abokin aikinsu ba.

Ma su zanga - zanga, sanye da takunkumi fuska saboda annobar korona, sun fito bakin titi dauke da manyan takardu da ke kunshe da sakon 'a yi wa Floyd adalci', 'shi ma bakin mutum rai gare shi' da sauransu.

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Buhari bai taba mika ikon ofishinsa ga kowa ba - Fadar Shugaban kasa

A bidiyon da wani a gefen hanya ya nada, an ga Floyd, dan shekaru 40, babu ko riga a jikinsa yayin da dan sandan ya take masa wuya a kasa na tsawon fiye da minti biyar duk da ya na ta ihun korafi da neman ceto.

"Ka take min wuyana. Ba na iya numfashi...Mama. Mama", kamar yadda Floyd ke ihu a cikin bidiyon.

Daga bisani an ga Floyd ya yi laushi, ya daina magana, ba ya ko motsi, a yayin da 'yan sandan ke umartarsa "tashi ka shiga mota".

Likitoci sun tabbatar da mutuwar Floyd bayan an kai shi asibiti.

Bayan korar 'yan sandan, babban jami'in 'yan sanda na birnin Minneapolis, Jacob Frey, ya bayyana bacin ransa a kan abinda ya faru tare da bayyana cewa za a gurfanar da 'yan sandan a gaban kotu da tuhumar kisa.

Da ya ke magana a kan faifan bidiyon, Frey ya ce, "abinda na gani ba daidai ba ne, ta kowacce fuska aka kalle shi."

"Mun ga yadda fararen 'yan sanda su ka ci zarafin bakin mutum ta hanyar dira gwuiwar kafa a makogoronsa har na tsawon minti biyar.

"Bai kamata zama bakar fata ya jawowa wani rasa ransa a Amurka ba," a cewar Frey.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel