Mulki ya na hannun Ubangiji, idan ya so in koma kujera sai na koma – Obaseki

Mulki ya na hannun Ubangiji, idan ya so in koma kujera sai na koma – Obaseki

Mai girma gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce ya na da yaƙinin zai lashe zabe mai zuwa da za ayi. Gwamnan ya fadi hakan ne saboda ya san cewa “Ubangiji ke bada mulki.”

Godwin Obaseki ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin kalaci na ranar Laraba, inda ya bayyana cewa shi mutum ne mai son zaman lafiya ba mai tada zaune tsaye ba.

Obaseki ya ke fadawa gidan talabijin a yau, 27 ga watan Mayu, 2020: “Ni ba mai son tada rigima ba ne. Amma ina da tabbacin yadda na zama gwamna, haka zan koma kan kujera."

Gwamnan na jam’iyyar APC mai neman tazarce ya kara da cewa: “Ubangiji ya ba ni mulki. Idan Ya na so in koma gwamna, zan cigaba. Babu mutumin da ya isa ya taka mani burki.”

Yayin da ake jiran zaben gwamna a jihar Edo a watan Satumba, Godwin Obaseki wanda ya samu sabani da tsohon mai gidansa, ya ce: “Mulki ya na zuwa ne daga hannun Ubangiji.”

KU KARANTA: Rikicin gida: Gwamnonin PDP sun yi maza sun gana da Sule Lamido

Mulki ya na hannun Ubangiji, idan ya so in koma kujera sai na koma – Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki ba ya shiri da Adams Oshiomhole
Asali: UGC

Mista Obaseki ya na magana ne game da rigimar zabe, inda ya ce tun fil azal shi mutum ne wanda bai yadda a tada hatsaniya har a zubar da jinin wani domin a samu nasarar zabe ba.

“Mun kasance mu na kira ga zaman lafiya. Menene matsalolin jihar Edo? Abin da ya dame mu shi ne amfani da dukiyar al’umma wajen kawowa jiha cigaba.” Inji gwamna Obaseki.

Ya ce: “Wannan bai kamata ya kai ga zubar da jini ba. Ba za mu bari wani ya bamu tsoro ko mu karaya ba, saboda wasu su na tunanin cewa za su iya tafka magudi, su murde zabe.”

Da aka tambayi gwamnan ko ya yi amfani da dukiyar jama’a wajen hawa kujerar da ya ke kai, sai ya ce ya na da abokai masu dukiya kuma ya yi aiki karkashin kasa a gwamnatin baya.

“Saboda haka duk maganar da ake yi na cewa an yi amfani da dukiyar wasu…Na zama gwamna ne ta karkashin jam’iyya kuma ina godiya da hakan." Ya ce ko ya aka yi, zai yi nasara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel