INEC ta ce ta na sa ran a fara yin zabe da na’urorin zamani a 2021

INEC ta ce ta na sa ran a fara yin zabe da na’urorin zamani a 2021

A ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2020 hukumar INEC ta ce za ta zauna da majalisa da sauran masu ruwa da tsaki domin rage kudin da ake kashewa wajen shirya zaben cike gurbi.

Hukumar ta INEC mai shirya zabe za ta dauki wannan mataki ne ganin hukuncin da kotun koli ta zartar na cewa kuri’un da aka samu a zabe na jam’iyyar siyasar da ta shiga takara ne.

Haka zalika INEC ta lura cewa a kashi 10% na zabukan da aka gudanar domin cike gurbi ne jam’iyyar da ta fara lashe zaben a karon farko ta sha kashi a hannun wata jam’iyyar.

Hukumar shirya zaben mai zaman kanta a kasar ta kuma yi magana game da shirin somin-tabi na kawo na’urorin zamani wajen gudanar da zabe kamar yadda ake yi a wasu kasashe.

INEC ta na sa rai ba da jimawa ba za a rika zabe da na’urori a maimakon takardu da aka saba amfani da su. Sai dai hukumar ta ce wannan ba zai yiwu a zabukan Ondo da Edo ba.

KU KARANTA: Idan ana so a ci zabe a 2023, sai an rike Sule Lamido - PDP

INEC ta ce ta na sa ran a fara yin zabe da na’urorin zamani a 2011
Shugaban INEC da sauran Jami'ai a lokacin zaben 2019
Asali: Original

A watan Satumba da Oktoba ne za a shirya zaben gwamnoni a jihohin Ondo da Edo. Amma sai a shekarar 2021, INEC ta ke sa ran na’urori za su yi aiki a duk wasu manyan zabuka a kasar.

Jaridar Punch ta ce INEC ta bayyana wannan ne a wata takarda da ta fitar wanda ya yi bayani game da yadda za a rika gudanar da zabe a lokacin da ake fama da annobar Coronavirus.

Shugaban hukumar INEC na kasa, farfesa Mahmood Yakubu ya rattaba hannu a kan wannan takarda mai tsawon shafuka 17 da ta shiga hannun ‘yan jarida a cikin farkon makon nan.

Takardar ta bayyana cewa hukumar za ta yi amfani da na’ura, ta kuma yi kokarin yadda za a dauki hayar malaman zabe ba tare da mutane sun taba juna ba a daidai wannan lokaci.

Za a nemo malaman zabe ne a gida, za a dauki wadannan matakai ne domin kare lafiyar jama’a, hukumar ta ce za ta fitar da tsarin da mutane za su bi wajen kada kuri’a a rumfunan zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng