Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yabi tsohon Gwamna Sule Lamido

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yabi tsohon Gwamna Sule Lamido

- Jam’iyyar PDP da Gwamnoninta sun jaddada amannarsu ga Sule Lamido

- Gwamnan Bauchi ya nuna cewa duk sun yarda da irin kamun ludayin Sule

- Bala Mohammed ya ce akwai bukatar a rike Sule domin ayi nasara a 2023

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kungiyar gwamnoninta sun bada goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, wanda ya na cikin manyan jiga-jiganta.

Jaridar The Guardian ta rahoto gwamnonin PDP su na cewa har gobe Sule Lamido shugaban jam’iyya ne kuma daya daga cikin jajirtattun ‘yan siyasar da ake ji da su a Najeriya.

PDP ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2020. Wannan jawabi ya fito ta bakin gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed yayin da su ka kai masa ziyara.

Bala Muhammed ya yi magana ne a madadin shugaban gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal, sa’ilin da shi da wasu manyan PDP su ka ziyarci Sule Lamido a gidansa.

Rahoton ya ce gwamnan na Bauchi ya nuna PDP ba za ta yi gigin asarar basira da tunanin Sule Lamido a daidai lokacin da ta fara shiryawa lashe zaben shugaban kasa na 2023 ba.

KU KARANTA: Zaben Gwamnan 2020 ya na cigaba da raba kan Jam’iyyar APC a Edo

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yabi tsohon Gwamna Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido
Asali: UGC

Manyan jam’iyyar adawar sun kai ziyara jihar Jigawa ne bayan sun samu labarin rikicin da ke neman ya barke a jam’iyyar. Sule ya yi gwamnan jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015.

“Abokan aikinmu gwamnonin PDP sun ce in zo in tabbatar maka cewa har yanzu darajarka da martaba da kimarka a idanunsu ya na nan. Mu na kaunarka, mu na ji da kai.” inji Bala.

Gwamna Bala Mohammed ya kara da cewa: “Shi (Sule Lamido) ne fuskar jam’iyyar PDP da siyasar Najeriya. Mun zo ne mu lallabi shugabanmu da wasu su ke yunkurin su bata masa rai.”

A jawabin na sa a madadin sauran gwamnonin hamayya, Bala ya ce PDP ta na bukatar Sule Lamido wajen karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Da ya ke na sa jawabin, Sule wanda ya rike minista da gwamna a PDP, ya ce Ubangiji ya yi masa baiwa, don haka ya ke ganin lokaci ya yi da matasa za su mike, su karbi mulkin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel