Zaben Edo: Yaran Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki sun ja daga

Zaben Edo: Yaran Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki sun ja daga

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ana cigaba da jan daga tsakanin magoya bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ta tsakiya, Suleiman Wambai, ya ce zaben kato-bayan-kato ya kamata ayi wajen fito da ‘dan takarar gwamnan APC a jihar Edo.

Da ya ke magana da manema labarai a garin Lafia, Suleiman Wambai ya ce hakan ne abin da ya fi dacewa domin gudun abin da ya faru da ‘yan takarar APC a Zamfara ya auku a bana.

“Tsarin mulkin APC ya bada dama shugaban jam’iyya su zabi hanyar da za a bi wajen fito da ‘dan takara.” Don haka Wambai ya ce uwar jam’iyya ta zabi zaben kato-bayan-kato a Edo.

Za a fito da wanda zai rikewa APC tutar takarar gwamna a jihar Edo nan da 19 ga watan Satumba. Sai dai ana fama da rabuwar kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kudancin kasar.

KU KARANTA: Buhari ya na goyon bayan Gwamnonin Edo da Ondo su zarce - Oyegun

Yayin da wasu su ke tare da tsohon gwamnan Edo kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, akwai bangaren da ke mara baya ga magajinsa watau gwamna mai-ci a yau.

Shugaban APC na jihar Edo, Anselm Ojezua, ya maidawa Suleiman Wambai martani, ya na mai cewa maganar za ayi zaben kato-bayan-kato wajen fito da ‘dan takara ba gaskiya ba ne.

A daidai lokacin da Anselm Ojezua ya ke ganin Wambai bai da hurumin da zai yi magana da yawun bakin APC a Edo, shugaban ‘yan tawaren APC, David Imuse ya fadi akasin haka.

Kanal David Imuse ya na da ra’ayin cewa abin da Suleiman Wambai ya fada shi ne matakin da uwar jam’iyya ta zartar. Imuse ya na cikin manyan yaran Adams Oshiomhole a jihar Edo.

Haka zalika wani jigon APC, Chris Azebanmwan, ya ce matsayar Wambai ba ta ci karo da tsari da dokokin jam’iyyar APC ba. Kawo yanzu dai APC ba ta cin ma magana guda ba tukuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel