Mun yi ram da motoci 30 da su ka kubce daga Kaduna a iyakarmu – Jihar Kano

Mun yi ram da motoci 30 da su ka kubce daga Kaduna a iyakarmu – Jihar Kano

- Gwamnatin Kano ta cafke wasu motocin matafiya da su ka saci hanya

- Ganduje ya ce daga ciki akwai motocin da su ka fito daga jihar Kaduna

A yayin da dokar hana shiga cikin wata jiha ta ke aiki saboda annobar COVID-19, gwamnatin Kano ta ce ta kama wasu mutane da su ka nemi shigo mata daga cikin jihar Kaduna.

Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kara kaimi wajen hana miyagu shigowa Kano. A yau ne gwamnatin Kano ta ce ta yi kamen wasu motoci daga jihohin da su ke makwabtaka.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano, Abba Anwar ya bada sanarwar cewa jami’ai sun kama wasu motoci fiye da 30 da su ka nemi shigowa jihar daga Kaduna.

Kotun wucin-gadin da aka kafa a kan hanyoyin Kano a karkashin jagorancin Salisu Idris Sallama ya kama motoci har 45 a garin Kwanar-Dangora da ke iyaka tsakanin Kano da Kaduna.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya sha alwashin tare hanyar Kano ranar Sallah

Wadannan motoci sun yi yunkurin satar hanya su shiga cikin Kano. 30 daga cikinsu sun fito ne daga Kaduna, yayin da 10 su ka fiti daga jihohin Jigawa da wasu wuraren na dabam.

An kama su saboda sun saba dokar hana shiga gari, kuma sun nemi su kutso jihar Kano yayin da bikin idin sallah ya karaso. Sakataren mai girma gwamnan ya shaida wannan dazu.

Gwamnatin Kano ta yabawa jami’an tsaro da su ka yi wannan kokari, inda Abdullahi Ganduje ya kuma yi kira da su kara dagewa. Gwamnan ya ce za a cigaba da sa ido a kan iyakokin.

“Mu na lura da iyakokinmu, mu na sa ido. Jami’an tsaro su tabbatar masu garkuwa da mutane, zafin addini, fashi da makami, satar jama’a ba su shigo daga Kaduna ba.” inji gwamnan.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa: “Idan aka haramta tsallaka jiha, ya kamata mutane su fahimci ya zama dole su bi wannan doka.” Jawabin ya fito ne a ranar 21 ga watan Mayu, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel