Lawan ya na so gwamnati ta karbe wutar lantarkin da aka saidawa ‘Yan kasuwa
- Majalisa ta ce a fara tunanin karbe kamfanin wutar lantarkin da aka saida
- Ahmad Lawan ya kuma roki gwamnati cewa ka da ta kara kudin lantarki
- Sanatoci za su binciki duk kudin da aka kashe domin tada kamfanonin wuta
A ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2020, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta koma kan batun wutar lantarkin da aka saida a Najeriya.
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sake duba lamarin saida kamfanonin wuta da nufin ayi gyara ko kuma a rusa yarjejeniyar da aka yi shekarun baya.
Majalisar dattawan kasar ta kuma yi kira ga gwamnati ta daga shirin karin kudin wutan da za ta yi. A cewar majalisar karin kudi a wannan marra zai sake jefa ‘yan Najeriya cikin kunci.
Ahmad Lawan ya gabatar da jawabi a zauren majalisar inda jaridar Vanguard ta rahoto ya na cewa idan aka cigaba da tafiya a haka, sai ayi shekara goma ba a samu gyara a harkar ba.
KU KARANTA: Minista ya sallami Shugaban kamfanin wutar lantarki a Najeriya
Lawan ya koka cewa duk da tiriliyoyin kudin da gwamnatin tarayya ta narka a harkar wuta, har yau babu wani canji da aka samu. Ya yi tir da yadda kamfanonin ke gudanar da kasuwanci.
“Mun ba su kamfanonin samarwa da raba wuta, sannan kuma sai su fito su na neman kudi. Ina tunani ya kamata Najeriya ta fara tunanin rusa cinikin ko a soke yarjejeniyar ko-co-kam.”
“Idan mu ka bar shi a haka, watakila nan da shekaru goma ba za mu samu wuta ba." A jawabinsa, shugaban majalisar ya ce ba ayi nasara wajen mallakawa ‘yan kasuwa kamfanonin wutan ba.
“Mun sa rai abubuwa za su gyaru, su yi kyau. Kamfanonin DisCos ba za su iya ba mu wuta ba. Kamfanonin GenCos su na da na su kalubalen. Bai kamata mu cigaba da ba su kudi ba.”
Sanatan ya ke cewa idan har kasuwancin su ke yi da gaske, babu dalilin a rika shaka masu kudin gwamnati. Ya kara da cewa: “Ya kamata kwamitinmu su binciki tiriliyoyin da aka kashe”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng