COVID-19: Jihar Nasarawa ta dage dokar hana zuwa wuraren bauta

COVID-19: Jihar Nasarawa ta dage dokar hana zuwa wuraren bauta

Gwamnatin jihar Nasarawa ta dage hana zuwa wuraren bauta na makonni biyu da ta saka.

Ta sanar da hakan ne a shafinta na twitter inda ta ce ta dage dokar ne na tsawon makonni biyu.

"Labari da dumi-dumi! COVID-19: Nasarawa ta dage dokar hana zuwa wuraren bauta na tsawon makonni biyu."

"Wannan na daga cikin matsayar da aka samu bayan taron da aka yi masu ruwa da tsaki na jihar don duba matakai na gaba da za'a dauka don dakile yaduwar annobar Covid-19," kamar yadda jihar ta wallafa a shafinta na twitter.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince a ci gaba da gudanar da sallolin Juma’a da kuma sallar Idi, duk da gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar zaman gida a jihar.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta ba da umarnin tsawaita dokar kulle a Kano har na tsawon makonni biyu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mai korona ta haifi tagwaye a Legas (Hoto)

Mashawarcin gwamnan a kan sabbin hanyoyin sadarwa na zamani, Salihu Tanko Yakasai, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, ya ce a yanzu gwamnatin Kano ta sake nazari a kan dokar takaita zirga-zirga.

A baya dai an sassauta wa al'ummar Kano dokar kulle a ranakun Litinin da Alhamis na kowane mako.

Sanarwar da hadimin gwamnan ya wallafa a kan shafin sa na Facebook ta bayyana cewa, gwamna Ganduje ya sahalewa al'ummar Kano damar ci gaba da yin Sallolin Juma'a da Sallar Idi.

Ana sa ran Sallar Idi ta karamar Sallar bana za ta kasance a ranar Asabar ko Lahadi, duk dai ranar da ta kasance 1 ga watan Shawwal a kalandar Musulunci.

Tanko Yakasai ya ce gwamnatin ta yanke shawarar hakan ne bayan wata doguwar tattaunawa da tayi da manyan Malaman Musulunci na jihar guda 30 a fadar gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel