Rotimi Amaechi: Rashin aikin yi ne ya yi sanadiyyar fadawa ta cikin harkar siyasa

Rotimi Amaechi: Rashin aikin yi ne ya yi sanadiyyar fadawa ta cikin harkar siyasa

Ministan sufurin Najeriya, Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya bayyanawa ‘yan jarida yadda rashin aiki da zaman kashe wando ya yi sanadiyyar jefa sa cikin harkar siyasa ba don ya yi niyya ba.

Rotimi Amaechi ya yi hira da jaridar The Punch inda ya shaida cewa burinsa da farko a rayuwa shi ne ya zama ‘dan jarida ko kuma lauya, amma a karshe sai ya kare da zama ‘dan siyasa.

Tsohon gwamnan na Ribas ya ke cewa bai shiga siyasa domin ya kawo karshen matsalolin kasar nan ba. Ministan ya bayyana cewa a gaskiya zaman kashe wando ne kawai ya matsa masa.

“Mahaifina ‘dan siyasa ne, ya yi takarar kansila a lokacinsa. Amma duk da haka ni ban yi sha’awar siyasa saboda na zama shugaba ko kuma in yi maganin matsalolin Najeriya ba.”

“Na shiga siyasa ne saboda ba ni da aikin yi. Ina kuma zaton cewa kaddara ta yi aiki a nan. Inji Amaechi wanda ya rike kujerar shugabar majalisar dokoki, gwamna da minista a gwamnati.

KU KARANTA: Ministan kasa ya gindayawa Malaman Jami’a yarjejeniyar yajin aiki

Duk da irin nasarorin da Amaechi ya samu a siyasa, ya ce ba zai ba wani daga cikin ‘ya ‘yan cikinsa shawarar ya yi siyasa ba, a cewarsa ana yin siyasa ne ba tare da wata doka ba.

“Mutum sai ya zama namijin gaske sannan zai iya yin nasara a siyasar yaudarar Najeriya.” Amaechi ya fadawa jaridar Punch cewa zamba da cin amana ne su ka cika siyasar kasar.

Amaechi ya ce: “Siyasar Najeriya ba abu ba ce da zan ba yarona shawarar ya shiga, saboda babu doka. Za a iya ruguza mutum cikin sauki. Sai mutum ya taki sa’a sannan zai kai labari.”

Ministan ya kara da cewa: “Ku na ganin abin da ake yi a Ribas yanzu, matasan da Ubangiji ya ba sa’a su na juyawa junansu baya. Da Ubangiji ba ya tare da ni, da yanzu an manta da ni.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel