Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari wani gari a jihar Adamawa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari wani gari a jihar Adamawa

'Yan ta'adda sun kara kai hari wani gari a jihar Adamawa washegarin ranar da aka yi rikici tsakanin wasu kabilu a jihar.

Lamarin ya faru ne a yankin Mbemun, garin da ya yi suna wajen sana'ar kifi a karamar hukumar Lamurde ta jihar.

Tashin hankalin ranar Juma'a ya faru ne a garin Tigno da ke karamar hukumar Lamurde ta jihar.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, mazauna yankin sun ce 'yan ta'addan sun kutsa garin dauke da makamai a ranar Asabar inda suka bankawa wasu gidaje wuta.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari wani gari a jihar Adamawa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari wani gari a jihar Adamawa
Source: UGC

"Sun kawo harin a sa'o'in farko na yau Asabar kuma mazauna garin sun ci gaba da neman wajen buya don kariya ga rayukansu," Bandrus James ya sanar da manema labarai yayin da yake kokarin tserewa.

"A yanzu ba zan iya cewa ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ba," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce 'yan sandan kwantar da tarzoma sun nufi garin don kwantar da hatsaniyar.

"A halin yanzu da nake magana, kwamishinan 'yan sanda, gwamna da sauran shugabannin tsaro na jihar na kan hanyar zuwa yankin," yace.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta bada dalilin da yasa Buhari ba ya saka takunkumin fuska

A baya mun ji cewa hukumar 'yan sandan Najeriya, shiyar jihar Adamawa, Arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da labarin ɓarkewar rikicin tsakanin wasu kabilu biyu a garin Tinno, karamar hukumar Lamorde na jihar.

Rahoton ya bayyana cewa an samu barkewar rikicin ne tsakanin Hausawa mazauna garin da kabilar Chobo, kuma ana tsoron cewa mutane da dama sun halaka.

BBC ta ruwaito daga wasu mazauna garin cewa wani dan karamin saɓani aka samu sakamakon buge wani ɗan ƙabilar Chobo da wani matashi bahaushe yayi.

Saboda haka `yan uwan wanda aka kade da babur suka far ma mai babur ɗin, inda wasu kuma daban sukayi kokarin kare shi, kawai sai rikici ya yi kamari.

Wani mazaunin garin, Sulaiman Bello, ya shaida cewa "Muna cikin mawuyacin hali saboda yanzu an yi mana ƙawanya ko ta ina kana jin ƙarar bindigogi kawai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel