Gwamna Ganduje ya gana da Sarakunan Kano a game da yaki da annobar COVID-19

Gwamna Ganduje ya gana da Sarakunan Kano a game da yaki da annobar COVID-19

A ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020, mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi wata ganawa ta musamman da duka sarakunan da ke kasar Kano.

An yi wannan taro ne a dakin taron Africa House da ke gidan gwamnati. Rahotannin da mu ka samu daga shafin ma’aikatar lafiya na Tuwita, sun ce manyan jihar sun halarci taron.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta bada labarin yadda wannan zama ya kasance, inda ta ce an tattauna tsare-tsaren da gwamnatin Ganduje ta kawo na yaki da cutar COVID-19 a jihar.

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro akwai sakataren gwamnatin Kano, kwamishinan lafiya, da Farfesa Abdussalami sannan sai ‘yan tawagar ma’aikatar lafiya daga Abuja.

Jami’an lafiyan Kano sun halarci wannan zama na musamman da aka yi da Sarakunan na Bichi, Rano, Karaye da Gaya da na cikin Kano yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19.

KU KARANTA: Gwamnati ta nada sabon Sarkin Rano bayan mutuwar Autan Bawo

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zanta da sarakuna: Aminu Ado Bayero, Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Ibrahim Abdulkadir da kuma Kabiru Muhammadu Inuwa.

A wajen wannan zama, kamar yadda mu ka samu labari daga shafin HRHBayero, Aminu Ado Bayero ya jagoranci addu’ar da aka yi wa tsohon sarkin Rano, Abubakar Tafida Ila.

Idan ba ku manta ba Ambasada Abubakar Tafida Ila ya rasu ne kwanakin baya ya na kan karagar mulki. Tuni aka nada Mai martaba Kabiru Inuwa a matsayin sabon sarkin Rano.

Gwamnan jihar Kano ya ke cewa: “Da wannan zama da aka yi, na tabbata mu na magana ne da dukkan sarakuna, da hakimai, da dakatai da masu unguwanni da limamai da kuma lawanai.”

Shugaban masarautar jihar Kano, mai martaba Aminu Ado Bayero, shi ne ya yi jawabi a madadin sauran sarakunan, inda ya tabbatar da cewa za su cigaba da ba gwamnatin jihar goyon-baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel