Goman karshe: Gwamna Zulum ya roki alfarma daya wurin jama'arsa

Goman karshe: Gwamna Zulum ya roki alfarma daya wurin jama'arsa

Ganin cewa da yawa daga Musulmi za su karkata addu'o'in su a kan annobar Coronavirus, Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya yi kira ga 'yan jihar da su dage wajen addu'a.

Ya bukaci su karkatar da addu'arsu a kan Boko Haram da masu daukar nauyin su a sallolinsu na Tahajjud a kwanakin karshe na watan Ramadan.

Gwamna Zulum ya bukaci addu'ar ne a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis wacce mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau ya fitar.

"Da yawa daga cikin Musulmi a fadin duniya za su dukufa addu'a ne a kan annobar nan da ta damu duniya.

"Babu shakka annobar babba ce kuma tana daga cikin manyan abubuwan da suka taba takura dan Adam a tarihinsa. Ina kira ga Musulmin Najeriya ballantana na jihar Borno da sauran yankin arewa maso gabas, da kada su manta da Boko Haram a cikin addu'o'in su.

Goman karshe: Gwamna Zulum ya roki alfarma daya wurin jama'arsa
Goman karshe: Gwamna Zulum ya roki alfarma daya wurin jama'arsa Hoto: Governor Borno
Asali: Twitter

"Annoba biyu ce ke damun mu kuma suna barna ba kadan ba. Akwai korona kuma akwai Boko Haram. Ku taya addu'ar Allah ya karya Boko Haram da masu daukar nauyin ta a duk inda suke a duniya.

"Kada mu manta da yi wa kanmu da junamu addu'a. Babu cutar da bata san magani, kuma muna fatan Allah zai bamu maganin abinda ke damun mu," takardar da Zulum yasa hannu ta bayyana.

Gwamnan ya kara da cewa: "Addu'a a kan Boko Haram tamkar dole ce a wannan lokacin. A yayin da dakarun sojin mu da sauran jami'an tsaron ke kokarin bamu kariya, addu'a ce kadai za mu iya taimakon su da ita.

"Wadannan sojojin da kuma 'yan sa kai suna matukar kokari kuma bamu da bakin da za mu iya musu godiya. Addu'ar mu suke bukata don ci gaba da samun nasara," ya kara da cewa.

KU KARANTA KUMA: Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe

Gwamna Zulum ya yi kira ga mutanen da suke da rufin asiri kuma za su iya tallafawa mabukata da su daure wajen taimakon marayu, masu takaba, 'yan uwa da makwabta a wannan watan mai alfarma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel