Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace babban hafsin soja

Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace babban hafsin soja

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani sojan Najeriya a kan hanyar Auga zuwa Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta arewa maso gabas ta jihar Ondo.

An gano cewa sojan na tafiya ne shi kadai a cikin motarsa yayin da 'yan bindigar suka damke shi tare da shigewa daji da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin din Channels.

Ya ce sojan da aka sace ya kai mukamin kaftin wato mai anini uku kenan.

Yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Ibadan yayin da 'yan bindigar suka sace shi a Auga Akoko.

Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace babban hafsin soja
Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace babban hafsin soja Hoto: Channels Television
Asali: UGC

"Sun shigar da shi daji amma sun ba shi damar waya da 'yan uwansa wadanda suka garzaya tare da sanar da ofishin 'yan sanda da ke yankin Ikare-Akoko.

"Amma kuma abun takaicin shine yadda kafin 'yan sanda su isa yankin, 'yan bindigar sun sauya mishi wuri. An samu motarsa da suka bari a wurin."

Ikoro ya jaddada cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Undie Adie ya bada umarnin yin bincike sosai don ceto Kaftin Gana.

Ya yi kira ga 'yan jihar masu matukar kare dokokin da kada su tsorata don za su samu isasshen tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.

KU KARANTA KUMA: Mace-mace: FG ta tura kwararru jihohin Katsina, Jigawa da Bauchi

A wani labarin na daban, mun ji cewa a kalla mutane 13 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai wani asibiti dake garin Kabul na kasar Afghanistan, daga ciki har da jarirai 2.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito kakaakin ma’aikatan cikin gida, Tareeq Arian ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace asibitin da aka kai harin na masu haihuwa ne.

Yan bindiga uku ne suka far ma asibitin, kuma suka rike asibitin tsawon sa’o’i kafin jami’an tsaro su samu nasarar kashe su duka, sa’annan suka tseratar da jariran dake cikin asibitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel