Mace-mace: FG ta tura kwararru jihohin Katsina, Jigawa da Bauchi

Mace-mace: FG ta tura kwararru jihohin Katsina, Jigawa da Bauchi

A ranar Talata gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta tura wakilanta na ma'aikatar lafiya zuwa Azare da ke jihar Bauchi, Katsina da Jigawa sakamakon hauhawar yawan mace-macen da ke aukuwa wadanda ake danganta wa da cutar coronavirus.

Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya sanar da hakan a garin Abuja yayin tattaunawa da kwamitin fadar shugaban kasar na yaki da annobar COVID-19.

"Wakilai daga ma'aikatar lafiya ta tarayya sun isa jihar Bauchi don binciken hadin guiwa tare da gwamnatin jihar a kan mace-macen da ke aukuwa a Azare.

"Wasu wakilan sun isa jihar Katsina da Jigawa don bincika abubuwan da jihohi ke bukata don dakile yaduwar annobar. Akwai bukatar dakina gwaji wadanda rashinsu ke kawo koma baya a fannin gwajin kwayar cutar.

"Sauran yankunan da ke fama da barkewar cutar duk za a mika musu tallafin da suke bukata.

"A kan wannan ci gaban, dole in jinjinawa kokarin kungiyar gwamnonin arewa da suke taimakon juna, tallafawa ma'aikatan lafiya da kuma wasu jihohin yankin da cutar ta fi kamari," Ehanire yace.

Mace-mace: FG ta tura kwararru jihohin Katsina, Jigawa da Bauchi
Mace-mace: FG ta tura kwararru jihohin Katsina, Jigawa da Bauchi Hoto: Federal Ministry of Health, Nigeria
Asali: Twitter

Ya jinjinawa gwamnonin jihohin Legas da Ekiti a kan yadda suke matukar kokari.

Ya ce, a safiyar Talata, an tabbatar da kamuwar sabbin mutum 242 a Najeriya. Hakan ya kai jimillar masu cutar zuwa 4,641 a jihohi 34 na kasar nan da birnin tarayya. Ya ce mutum 150 ne cutar ta kashe a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa, mutum 902 ne aka yi musu magani tare da sallamarsu daga asibiti.

KU KARANTA KUMA: Ba zan iya auran mutum irin Dangote ba – Jarumar fim

"Ma'aikatar lafiya ta tarayya na aiki da wasu cibiyoyi, bangarorin gwamnati da wasu kungiyoyi don ganin nasarar dakile yaduwar cutar.

"Ma'aikatar lafiyar na ci gaba da kula da halin da wasu jihohi ke ciki, inda annobar ta samu wurin zama. Mun shawo kan matsalar jihar Kano ta hanyar tura kwararru.

"Ina farin cikin sanar da ku cewa kungiyar ta yi matukar kokari a aikin da aka tura ta kuma tana taimakawa wurin samo daidaituwa a bangaren kiwon lafiyar jihar," ministan ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel