Kwamred Sani ya ce Azikiwe ya na cikin Shugabannin kirkin da aka taba yi

Kwamred Sani ya ce Azikiwe ya na cikin Shugabannin kirkin da aka taba yi

Shararren ‘dan siyasar nan na jihar Kaduna, Kwamred Shehu Sani ya yi magana game da shugabannin Najeriya, inda ya zabi guda daga cikinsu ya rika sharara masa yabo.

A cewar Shehu Sani, duk cikin tsofaffin shugabannin da aka yi a tarihi, babu wanda ake yi wa kallon ‘dan kishin kasa wanda bai sa kabilanci a siyasa ba irin Nnamdi Azikiwe.

Sanata Shehu Sani ya fito shafinsa na Tuwita ya rubuta:

“Har gobe mafi yawan ‘yan Najeriya da aka yi a da da wadanda su ke nan a yau, su na daukar Cif Nnamdi Azikiwe a matsayin wanda bai da akidar bangaranci da kabilanci.”

Duk da irin yabon da Shehu Sani ya yi wa Azikiwe, marigayin bai samu damar yin mulki ba. Ya yi takarar shugaban kasa sau da-dama amma bai kai ga nasara ba har ya mutu.

Sani ya ke cewa game da Azikiwe: “Asalin ‘dan kishin kasa ne mai kaunar nahiya Afrika wanda irin tafiyar siyasarsa kila ba za ta burge kasar da aka saba nuna rabuwar kai ba.”

KU KARANTA: Dalilina na janye jiki daga harkar siyasar Najeriya - Jonathan

Kwamred Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas ya yi wannan magana ne a ranar bikin cika shekara 24 da rasuwar tsohon shugaban.

Nnamdi Azikiwe ya rasu ne a rana irin ta jiya, 11 ga watan Mayu a 1996. Azikiwe ya na cikin wadanda su ka yi fafutuka wurin karbowa Najeriya ‘yanci a hannun Birtaniya.

Bayan nan kuma Sani ya tofa albarkacin bakinsa kan batun da Goodluck Jonathan ya yi na cewa ya rabu da siyasa. Sani ya ce shugabannin baya sun fadi irin wannan sun saba.

“IBB ya ce ya daina siyasa, daga baya ya sake shigowa harkar. OBJ ya taba cewa ya daina siyasa, ya dawo ya marawa ‘dan takara baya, sannan ya sake komawa.”Inji Sanatan.

“Buhari ya taba cewa ya ajiye siyasa, ba zai sake takara ba, amma ya dawo. Atiku ya taba cewa ya kai karshen tafiyarsa, amma ya lallabo. Anya Jonathan?” Sani ya tambaya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel