Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta zauna da Uzor Kalu bayan fitowansa daga dauri

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta zauna da Uzor Kalu bayan fitowansa daga dauri

- Orji Uzor Kalu zai koma bakin aikinsa a Majalisa bayan ya samu ‘yanci

- Sanata Orji Kalu ya fito daga gidan yari ne bayan watanni biyar a daure

- Kalu ya yi alkawarin kawo dokokin da za su sa a gyara kurkukun kasar

Idan har abubuwa ba za su sake zani ba, sanatan da aka saki daga gidan kurkuku a ranar Juma’ar da ta gabata watau Orji Uzor Kalu, zai zauna a majalisa tare da abokan aikinsa a makon nan.

Orji Uzor Kalu ya samu ‘yanci ne a makon jiya bayan alkalin kotun koli ya ruguza shari’ar da aka yi masa. Kotun ya ce alkalin da ya yankewa sanatan dauri bai da hurumin zama a shari’ar.

Daily Trust ta ce Orji Uzor Kalu wanda ya yi gwamna a jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007 zai cigaba da aikinsa a majalisar dattawa har sai lokacin da aka karkare sabuwar shari’a da shi.

Sanata Uzor Kalu ya shafe watanni biyar da ‘yan kwanaki a gidan yarin Kuje bayan an same shi da laifin karkatar da wasu Naira biliyan 7.6 daga asusun gwamnati a lokacin ya na mulki.

KU KARANTA: EFCC: Sanata Orji Uzor Kalu ya samu 'yanci daga gidan kurkuku

Jaridar Daily Trust ta ce a lokacin da Orji Uzor Kalu ya ke zaman kason shekaru 12 a gidan kurkuku, ya na karbar albashinsa da duk wasu kudi a matsayinsa na ‘dan majalisar tarayya.

Majalisar ta ki bada damar wani ya maye gurbinsa, kakakin majalisar ya ce sanatan na APC zai cigaba da karbar albashi duk da cewa ba ya aiki har sai an ga karshen shari’arsa a kotun koli.

A lokacin da ya ke tsare a gidan kurkuku, mataimakin shugaban masu tsawatarwa, sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya maye gurbin Uzor Kalu, a gobe ake sa ran sanatan zai dawo matsayinsa.

Sakin Orji Uzor Kalu ke da wuya, ya tabbatarwa Duniya zai koma bakin aikinsa da zarar an bude majalisar tarayya. A ranar Talata irin ta gobe ne dai ‘yan majalisa su ke fara zama a Najeriya.

Sabon ‘dan majalisar ya ce ya koyi muhimman darasi a zaman watanni biyar da ya yi gidan yari. Kalu ya yi alkawarin kawowa majalisa kudirori da za su taimaka wajen gyara gidajen yari.

Rabon Kalu da majalisa tun farkon watan Disamban bara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel