Mai dakin Sanusi II, Saadatu Barkindo Mustapha ta haifi 'Yar Yarinya

Mai dakin Sanusi II, Saadatu Barkindo Mustapha ta haifi 'Yar Yarinya

- Amaryar tsohon Sarki Malam Muhammadu Sanusi II ta haihu kwanan nan

- Tsohuwar Sarauniyar Kano Saadatu Barkindo Mustapha ta haifi 'Ya mace

- Saadatu Barkindo ta tare a gidan Sanusi II ne bayan shekaru 4 da aurensu

Ana rade-radin cewa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya samu karuwa bayan matarsa ta karshe watau Hajiya Saadatu Barkindo Mustapha ta haifi ‘diyar farko da mai martaban.

An sanar da haihuwar mai martaba ne a wani shafin Tuwita na @MSII_dynasty. Legit.ng ba ta da tabbacin cewa tsohon sarkin na kasar Kano ya san da zaman wannan shafi na masoyansa.

Shafin masoyan mai martaban sun rubuta: “Gimbiyarmu ta iso.” Ba a bayyana sunan jaririyar ba, duk da akwai wata takarda a hannun da ke nuna bayani game da lokacin da aka haife ta.

Saadatu Barkindo Mustapha ta tare a gidan mai martaban ne a shekarar bara war haka. A lokacin da ‘diyar Lamidon ta Adamawa ta auri tsohon sarkin Kano ta na da shekara 18 ne a 2015.

KU KARANTA: Lokacin da Sarki Sanusi II zai bar Kano bayan Ganduje ya tsige shi

Sarauniya Saadatu Barkindo Mustapha ba ta tare a wancan lokaci ba har sai bayan da ta kammala karatu. Idan ba za ku manta ba wannan aure ya jawo ce-ce-ku-ce a wancan lokaci.

Sanusi II ya samu wannan karuwa ne kusan bayan shekaru 20 cif da rasuwar mahaifinsa. Ciroman Kano, Malam Aminu Lamido Sanusi II ya rasu ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2020.

Jaridar Daily Times ta ce wasu daga cikin na kusa da Sanusi sun tabbatar da wannan haihuwa da aka yi masa. Ana tunanin cewa wannan jaririya ce ‘diyar tsohon sarkin ta 25 a Duniya.

Kwanakin baya wani dattijon Arewa Dr. Junaidu Mohammed ya bayyana cewa Sanusi II ya na da ‘ya ‘ya 24. Sauran matan Mai martaban su ne Sadiya Ado Bayero, Hajiya Maryam, da Rakiya.

A daidai lokacin da iyalin Sanusi II su ke murna, mun samu labari a wannan shafi na @MSII_dynasty cewa a kasar Kano an yi rashin ‘Dan Iya, Faruk Bayero wanda ya rasu jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel