Kungiyar ASUU ta yi magana game da tsarin IPPIS, yajin aiki da harkar ilmi

Kungiyar ASUU ta yi magana game da tsarin IPPIS, yajin aiki da harkar ilmi

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi wata hira ta musamman da Legit.ng, inda ya tabo batutuwa da su ka shafi harkar ilmi da gwamnatin tarayyar Najeriya.

Biodun Ogunyemi ya bayyana dalilan da su ka sa malaman jami’a su ke adawa da manhajar biyan albashi na IPPIS, a cewarsa tsarin zai hana jami’o’i damar daukar malamai na musamman.

Wata matsala ta IPPIS ita ce za ta maida jami’a tamkar sauran ma’aikatun gwamnati, wanda ya ci karo da yadda aka san su a ko ina. sannan IPPIS za ta tubewa jami’o’i ikon da su ke da shi.

A game da yawan shiga yajin aiki, Ogunyemi ya zargi gwamnatin tarayya da sabawa alkawuran da su ka dauka. Shugaban na ASUU ya ce su na yin yaji ne domin su ceci harkar ilmin kasar.

Farfesan ya ce a dalilin kokarinsu ne gwamnatin tarayya ta kafa hukumar TETFund a 1992. Ya ce daga cikin asusun TETFund ne aka zari kudin da aka bude sababbin jami’o’in tarayya a 2011.

KU KARANTA: ASUU: Dole Malaman Jami'a su gabatar da BVN kafin su samu albashi

Kungiyar ASUU ta yi magana game da tsarin IPPIS, yajin aiki da harkar ilmi
Shugaban Kungiyar ASUU ya ce IPPIS zai cirewa Jami'a karfin iko
Asali: Facebook

Shugaban na ASUU ya yi magana game da hana su albashi da aka yi na fiye da watanni uku. Ogunyimi ya nuna cewa ba su jin tsoron horon da ake yi masu da yunwa domin tuni sun saba.

ASUU ta ce tsofaffin shugabannin baya; Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da Sani Abacha duk sun taba hana su albashi har su ka taba shafe watanni shida.

Rabon da a biya mafi yawan malaman jami’a albashi tun a watan Junairu.Ogunyemi ya shaidawa Legit.ng cewa ko akwai albashi, ko babu albashi za su jajirce wajen cin ma matsayarsu.

Kungiyar ASUU ta tubure ta ce ‘ya ‘yanta ba za su gabatar da lambobin BVN dinsu a matsayin sharadin biyansu albashi ba. Kungiyar ta ce hakan bai taba zama sharadi a albashinsu ba.

Kamar yadda Ogunyemi ya bayyana, manhajar IPPIS ba ta bada damar daukar malaman aro ko masu gajerar kwangila wadanda ba a biyansu kudin fansho ba, don haka su ke adawa da shirin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel