‘Yaradua: Me Jama’a su ke fada shekara 10 da rasuwar tsohon Shugaban Najeriya

‘Yaradua: Me Jama’a su ke fada shekara 10 da rasuwar tsohon Shugaban Najeriya

A rana irin ta jiya a 2010 Ummaru Musa ‘Yar’adua ya kwanta dama. Hakan na nufin shekaru goma kenan da Najeriya ta yi rashin shugaban ta na 13 a tarihi kuma na biyu bayan 1999.

Mun tattaro abin da mutane ke fada game da Alhaji Ummaru Musa ‘Yar’adua a shafukan sada zumunta na Tuwita. Kusan duk jama’a dai suna fadin alheri ne a kan tsohon shugaban kasar.

Ga kadan daga cikin abin da mutane ke cewa:

Ameenu Kutama ya rubuta: “Shekaru goma da su ka wuce mu ka farka da rasuwar asalin ‘dan kishin kasa, ma’aikacin gwamnati, wanda ya san shugabanci, mu ka bizne shi, har yau ba mu wartsake daga rashinsa ba. Allah ya kara maka hutu, mafi kyawun shugaban da mu ka yi, Umaru Musa Yaradua.”

"Ya na cikin nagarin shugabannin da mu ka yi a shekarun nan. Ya yi farin jini a wajen mafi yawan ‘Yan Najeriya, mutum mai nagarta. Allah ya jikansa da rahama." – Hafsah Amally

"Shekaru goma kenan da Najeriya ta rasa shugaban kwarai, ‘dan siyasa, ‘dan kishin kasa, mai neman zaman lafiya da hada-kan kasa, mai kaunar ‘Yan Najeriya, wanda ya ke da aniyar gyara da niyyar kwarai na kawo sauyi. Umaru Musa Yar'adua."

Sola Kuti ya rubuta: “A ranar da tsageru su ka zo ganawa da shugaba ‘Yar’adua, ya kwanta rashin lafiya. Hadimansa su ka fada masa cewa Jonathan zai iya ganawa da su. Sai ya ce na yi masu alkawari, don haka dole in cika masu, ya kuma gana da su. A dalilin wannan kawai gangar man da Najeriya ta ke hakowa ya karu washegari.”

KU KARANTA: Abubuwan da 'Yaradua ya yi da ya sha ban-ban da sauran Shugabanni

Shi ne wanda ya fi kowane shugaba da kasar nan ta yi. - Olalekan Sylvester

Shi kuwa Jamilu Ibrahim Ahmed cewa ya yi: “Marigayi Umaru Musa ‘Yaradua ne babban rashin da Najeriya ta yi tun da aka fara mulkin farar hula. Shekaru goma kenan yanzu da tafiyarsa. Shugaba wanda ya ke da aniya da hangen nesar gyara kasa. Allah ya masa rahama, ya ba shi AljannaFirdausi. Aamiin!”

"A cikin kankanin lokaci ka sa ‘yan Najeriya su ka san menene gwamnatin jama’a, ta jama’a kuma domin jama’a. Kowa ya kaunace ka ba tare da la’akari da bambancin yanki, addini ko kabila ba domin ka yi abin da ya dace a mulkin ka." Inji Ibikunle Felix.

Shi kuma Anas Zurmi ya jero irin jerin ayyukan da shugaban ya yi ne a lokacin da ya ke mulki.

Wani Matashi daga Katsina mai suna, Isah Miqdad ya ce: "A yakin neman zaben 2003, Marigayi ‘Yar’adua ya daga hannun mahaifina ya ce: “Kuri’ar da aka ba Miqdad AD Saude, kuri’ar Ummar Musa ‘Yar’adua ce. Yau dukkansu ba su nan. Allah ya yi wa wadanda mu ke kauna rahama."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel