Duk mun ji kunya – Dino Melaye ya caccaki yan siyasa, ya ce dukkaninsu sun gaza

Duk mun ji kunya – Dino Melaye ya caccaki yan siyasa, ya ce dukkaninsu sun gaza

- Shahararren dan siyasan Najeriya, Dino Melaye, ya je shafin soshiyal midiya domin ya caccaki kansa da takwarorinsa a gwamnati

- A cewar Melaye, kasar na siyar da danyen man fetur tsawon shekaru 64 amma ta gaza ciyar da al’ummanta na mako biyu

- Dan siyasan ya bayyana cewa duk wanda ya riki ko yake rike da mukamin siyasa a kasar, harda shi kansa, duk sun gaza

Annobar coronavirus da ta shigo duniya ta sauya abubuwa da dama ta hanyoyin da mutane basu zata ba.

Kasashe da daman na fafutukar ganin sun kula da al’ummansu da kokarin rage masu damuwa ta hanyar samar da tallafi saboda kada su damu sosai kan batun zamansu a gida.

Lamarin ya sha bambam ga wasu kasashe da dama ciki harda Najeriya. A yanzu gwamnati ta dage dokar hana fita domin mutane su samu damar fita wajen harkokinsu na yau da kullum da kuma ciyar da kansu.

Dan siyasan Najeriya, Dino Melaye, ya je shafin soshiyal midiya domin caccakar takwarorinsa a gwamnati. A cewar tsohon sanatan, duk wani da ya riki ko yake rike da mukamin siyasa a kasar ya gaza.

Ya ci gaba da bayanin cewa Najeriya ta siyar da danyen man fetur tsawon shekaru 64 amma ta gaza ciyar da al’ummanta na makonni biyu a lokacin da aka rufe kasar.

Dino Melaye ya kuma bayyana cewa Ubangijin talaka zai yi musu hisabi.

A rubutun da ya wallafa, ya rubuta: “Dukkanmu mun ji kunya.”

“Duk wani mutum da ya riki ko yake rike da mukamin siyasa a Najeriya imma na takara ko na nadi harda ni kaina duk mun gaza. Mun siyar da danyen man fetur tsawon shekaru 64 amma mun gaza ciyar da al’ummanmu na tsawon makonni biyu kacal da aka rufe kasa!!! Kusani, Ubangijin talaka zai yi mana hisabi dukkanmu. Lokaci ya yi da za a sake tunani.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa Sanata Dino Melaye ya shigar da karar kakaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila gaban kotu kan kudurin dokar hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa, NCDC.

Hukumar NCDC ita ce hukuma daya tilo dake kan gaba wajen yaki da annobar cutar Coronavirus a Najeriya a yanzu haka, cutar da ta kama fiye da mutane 2,500 ta kashe fiye da 80.

Hakan ta sa kakaakin majalisa, Femi Gbajabiamila ya gabatar da kudiri a gaban majalisa da za ta baiwa gwamnati ikon amfani da duk wani gida a kasar nan don killace masu cutar.

Sai dai Dino ya kalubalanci kudurin, don haka ya maka kakaakin, ministan sharia Abubakar Malami, sufetan Yansanda Muhammadu Adamu da akawun majalisun dokoki gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel