Kungiyar SERAP ta bukaci Hukuma ta fito da Lawal Izala da wasu mutum 2 a Katsina

Kungiyar SERAP ta bukaci Hukuma ta fito da Lawal Izala da wasu mutum 2 a Katsina

- Kwanaki ‘Yan Sanda su ka kama wani Bawan Allah da ya fito ya na zagin Shugabanni

- Kungiyar SERAP ta bukaci a saki wannan Dattijo tare da duk sauran wadanda aka kama

Kungiyar nan ta SERAP mai kokarijn kare hakkokin mutane ta yi magana game da wani tsoho ‘dan shekara 70 da aka kama bisa laifin zagin shugaban kasa da gwamnan jihar Katsina.

SERAP ta yi kira ga ‘yan sanda da gwamnatin Najeriya da su yi maza su saki wannan mutumi ba tare wani sharadi ba. Kungiyar ta kuma bukaci a fito da sauran mutane biyu da aka kama.

A wani jawabi da kungiyar mai zaman kanta ta yi, ta nemi hukumomi su fito da Lawal A. Izala mai shekara 70 da kuma Bahajaje Abu da Hamza Abubakar da ke hannun ‘jami’an tsaro.

An kama wannan tsoho ne tare da Bahajaje Abu da Hamza Abubakar masu shekarau 30 da 27 da zargin fitowa su na zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Aminu Masari.

Da aka tambayi Izala kan abin da ya sa ya zagi mai girma shugaban kasa da kuma gwamnan jihar Katsina, sai ya bayyana cewa an sace masa dabbobi ne bayan an kashe masa yaron kiwo.

KU KARANTA: Masu yi wa Likitoci karya game da Coronavirus za su shiga kotu da Gwamnati

Ganin cewa ya rasa dukiya da yaron aikinsa, Malam Lawal Izala ya fito cikin fushi ya na tikarawa shugabannin zagi a gaban Duniya. A dalilin wannan ne ‘yan sanda su ka yi ram da shi.

SERAP ta ce zagin shugaba Muhammadu Buhari da Aminu Bello Masari bai isa ace ya sa an kama mutum an tsare ba. Kungiyar ta ce za ta kai kara kotu idan aka cigaba da tsare mutanen uku.

“Za mu kalubalanci wannan sabawa doka a kotu idan ba ayi maza an sake su ba. Kama mutum da laifin zagi ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa da dokokin kare hakkin Bil Adama.”

“Shugabanni masu rike da manyan mukaman iko za su iya samun kansu a sukar jama’a. Maganar gaskiya ita ce kalaman da ake zargin cewa zagi ne ba su isa su sa a kai ga tsare mutum ba.”

Kungiyar ta SERAP ta kara da cewa: “Mahukuntan Najeriya su girmama, mutunta, sannan su yi kokarin kare damar mutane ta fitowa su fadi duk irin abin da ransu ya ke so a kasar nan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel