Nyesom Wike zai kai gwamnati kara a dalilin zaran kudi daga asusun FAAC

Nyesom Wike zai kai gwamnati kara a dalilin zaran kudi daga asusun FAAC

- Gwamnatin Ribas za ta shiga kotu da gwamnatin tarayya a Najeriya

- Gwamna Nyesom Wike zai kalubalanci kudin da aka zara daga FAAC

- Wike ya ce bai kamata a zari kudin ba tare da tuntubar duk Jihohi ba

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa zai dauki mataki game da zarar kudi da gwamnatin tarayya ta yi daga asusun FAAC ba tare da ta tuntubi gwamnonin jihohi ba.

Gwamna Nyesom Wike ya fara shirin gabatar da karar gwamnatin tarayya a kotu. Gwamnan zai kulubalanci gwamnatin tarayya a kan cire kudi har Naira biliyan 11 daga asusun tarayya.

Mista Nyesom Wike ya bayyana wannan ne a ranar Juma’a 1 ga watan Mayu, 2020. Gwamnatin tarayya ta zari wannan biliyoyin kudi ne domin aikin dakarun jami’an ‘yan sandan kasar.

Mai girma gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a jihar Ribas domin sanar da jama’a matakin da gwamnatinsa ta dauka na yaki da cutar COVID-19.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta hana Gwamnan Ribas kama Matukan jiragen sama

Nyesom Wike zai kai gwamnati kara a dalilin zaran kudi daga asusun FAAC
Wike ya ce ba rigima ta sa zai kai gwamnatin Buhari kotu ba
Asali: UGC

Wike ya ce gwamnatin jihar Ribas za ta bi sharudan da shugaba Muhammadu Buhari ya gindaya na bude harkar kasuwanci a sannu a hankali a fadin kasar domin gudun yada COVID-19.

A game da Naira biliyan da aka cire daga asusun gwamnatin tarayya na FAAC, aka mikawa ‘yan sanda, gwamna Nyesome Wike ya ce: “Lauyoyinmu za su shirya takardu, su tafi gaban kotu.”

Gwamnan ya nuna cewa jihohi su na da hakki a cikin kason FAAC: “Babu wanda ya ce ba za a goyi bayan ‘yan sandanmu ba, amma dole ka samu amincewar jihohi kafin ka dauki kudin.”

“Na fadawa shugaban gwamnonin Najeriya cewa jihar Ribas za ta kalubalanci wannan lamari a gaban Alkali. Ba wai batun fada da gwamnatin tarayya ba ne.” Inji gwamna Nyesom Wike.

Wike ya ce: “Jihata ta na da hakki a cikin wannan kudi, saboda haka dole a sanar da mutane. Ko ya shari’a ta kare a kotu, tarihi ya dauka cewa, na tsayawa mutanena da kuma gaskiya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng