Amurka, Ingila, Sin da kasashen da ke neman kwayan maganin da zai iya kashe COVID-19

Amurka, Ingila, Sin da kasashen da ke neman kwayan maganin da zai iya kashe COVID-19

Hukumar lafiya ta Duniya watau WHO ta tabbatar da cewa kawo yanzu babu wani magani da aka yi wanda ke warkar da cutar COVID-19. Sai dai akwai bincike rututu da wasu ke ta yi.

Daga cikin wadannan bincike da ake yi har an kai ga fara yin gwajin wasu magunguna da yanzu aka kirkiro. Amma wasu a bayan fage su na ikirarin cewa sun gano maganin wannan cuta.

1. Madagaska

Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya kaddamar da wani magani da kasar ta ke tunani zai iya maganin cutar COVID-19. Masana sun nuna alamar tambaya game da wanna magani.

Kungiyar masana kiwon lafiya na ANAMEM ta ce ana shan wannan magani ne kamar shayi.

2. Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya fito ya na neman hukumar FDA ta Amurka ta bada damar a rika amfani da kwayoyin hydroxychloroquine and chloroquine domin maganin COVID-19.

Wadannan magunguna sun dade a Duniya ana amfani da su wajen kashe zazzabin masassara.

3. Australiya/Sin

Wata cibiya da ke binciken lafiya a kasar Australiya ta na shirin fara gwajin wani magani da ake sa rai zai iya kashe kwayar cutar COVID-19. A kasar Sin aka fara kirkiro wannan magani.

4. Amurka

Wani magani da aka kirkiro a Amurka shi ne Remdesivir. An fara fito da wannan magani ne a 2014 lokacin da aka yi fama da Ebola. Sai dai ba ayi nasarar warkar da cutar Ebola da shi ba.

Yanzu ana yin wani sabon bincike da wannan magani, ana kuma sa ran a dace wannan karo.

KU KARANTA: Farfesan Najeriya ya ce ya na da maganin da zai warkar da masu COVID-19

Amurka, Ingila, Sin da kasashen da ke neman kwayan maganin da zai iya kashe COVID-19
Hukumomin Najeriya sun ce ayi watsi da maganin COVID-19 na bogi da ke kasuwa
Asali: Twitter

5. Amurka

Shekarun baya Amurka ta kirkiro wani maganin kanjamau; Lopinavir/Ritonavir. Ana saida wannan magani da sunan Kaletra a kasuwa. Ana sa ran kuma zai iya yin aiki a kan COVID-19.

Wani magani da ke cikin wannan sahu shi ne Arbidol wanda shi ma ake jarraba aikinsa.

6. Jafan

A 2014 kasar Jafan ta fito da maganin Favipiravir wanda ake amfani da shi wajen ciwon mura. Yanzu kasashe sun fara binciken ganin yiwuwar amfani da maganin a kan masu COVID-19.

7. Sin

Masu nazari a wani dakin bincike na Sinovac Biotech da ke birnin Beijing a kasar Sin sun yi nisa a yunkurin gano maganin COVID-19 har kuma an fara samun nasarar kashe cutar a jikin birai.

8. Ingila

Masanan da ake ji da su a jami’ar Oxford sun dukufa wajen gano maganin cutar COVID-19 nan da karshen shekarar bana. Wata cibiyar jami’ar ne ta ke wannan aiki tare da kamfanin AstraZeneca.

9. Najeriya

A Najeriya an samu kwararrun masana da su ke ikirarin sun gano maganin wannan cuta. Daga cikinsu akwai Farfesa Maurice Iwu, Farfesa Ayodele Adeyele da kuma Farfesa Joseph Akpa.

Sauran kamfanonin da ke wannan aiki a ketare sun hada da Moderna, Inovio, Johnson & Johnson. Akwai jami’o’i a kasashen Ingila da Australiya da ke kokarin gano maganin cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel