Yanzu-yanzu: Gidan tsauni mai hawa 8 ya rufto kan jama'a a Owerri

Yanzu-yanzu: Gidan tsauni mai hawa 8 ya rufto kan jama'a a Owerri

Wani gidan tsauni mai hawa takwas da kae gan ginawa ya rufto kan mutane da dama a Owerri, babbar birnin jihar Imo.

Ginin dake titin Yar’ Adua Drive ya rufto ne ranar Alhamis.

Channels TV ta ruwaito cewa yanzu haka ana kokarin tsamo mutane kimanin 25 da ta rutsa da su ciki.

Kawo yanzu dai a ceto mutane 15 amma abin takaici mutum daya ya rasa ransa.

Ku saurari cikakken rahoton....

Source: Legit

Tags:
Online view pixel