Coronavirus: Gwamna Masari ya sa ma wasu kananan hukumomi 3 takunkumi
Gwamna Aminu Bello Masari na jahar Katsina ya sanar da garkame kananan hukumomin Musawa, Kankia da kuma Matazu sakamakon bullar cutar COVID19.
Mai magana da yawun gwamnan, Abdulhadi Bawa ne ya sanar da haka a ranar Laraba inda yace dokar rufee garuruwan zai fara aiki ne daga ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, karfe 7 na safe.
KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal
Gwamnatin Katsina ta yanke shawarar rufe duk karamar hukumar da aka samu bullar cutar Coronavirus, tare da hana shige da fice a cikinta da zirga zirga don dakile yaduwar cutar.
Sanarwar ta ce zuwa yanzu an samu karuwar mutanen dake dauke da wannan cuta a jahar Katsina kamar haka;
Katsina – 2, Daura – 2, Dutsinma – 1, Kankia – 1, Musawa – 1, Matazu – 1 da Batagarawa –1
Kwamitin yaki da yaduwar Coronavirus a jahar Katsina ta bayyana cewa an samu mutane 6 da suka warke daga wannan cuta, kuma dukkaninsu sun fito ne daga karamar hukumar Daura.
Daga karshe sanarwar ta bayyana cewa kwamitin za ta sanar da wuraren da za’a rika sayayyan kayan abinci da kayan amfanin yau da kullum a kananan hukumomi uku da dokar ta shafa.
A wani labarin kuma, gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana mutuwar wasu mutane 3 daga cikin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar.
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka da tsakar daren Talata, 28 ga watan Afrilu, ta bakin hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Muhammad Bello.
Sanarwar ta ce: “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sakkwato ya sanar da mutuwar mutane 3 a sanadiyyar cutar COVID19, duka mamatan uku suna da tattare da wasu cututtuka dake damunsu kamar ciwon siga, ciwon asma da kuma hawan jini.”
A ranar 19 ga watan Afrilu ne jahar Sakkwato ta fara samun bullar cutar Coronavirus, a ranar 23 ga wata kuma aka samu mutum na biyu, a cikin kwanaki 10, har ta kama mutane 10, ta kashe 3.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng