Zamfara: An kama wasu mata biyu 'yan gida daya da ke yi wa 'yan bindiga leken asiri

Zamfara: An kama wasu mata biyu 'yan gida daya da ke yi wa 'yan bindiga leken asiri

Rundunar tsaro na NSCDC a jahar Zamfara ta kama wasu masu yi wa yan bindiga leken asiri su uku a karamar hukumar Anka.

Daga cikin masu leken asirin harda wasu mata biyu 'yan gida daya daga jumhuriyyar Nijar.

Jami’an rundunar da ke sintiri ne suka kama mutanen uku a hanyar Bagega da ke karamar hukumar Anka na jahar Zamfara bayan sun samu jawaban kwararru.

Kwamandan rundunar, Aliyu Garba ya ce namijin cikinsu Shafiu Abdullahi ya tona cewa yana taimaka wa “Shaho”, wani shugaban kungiyar barayin shanu da garkuwa da mutane wajen kai masa kayayyaki.

Zamfara: An kama wasu mata biyu 'yan gida daya da ke yi wa 'yan bindiga leken asiri

Zamfara: An kama wasu mata biyu 'yan gida daya da ke yi wa 'yan bindiga leken asiri
Source: UGC

Matan su biyu, Binta da Balki Hussaini, wadanda suka fito daga yankin Madawa da ke Kanni a Jumhuriyyar Nijar, sun kasance yan matan wani dan fashi mai suna Jijji, wanda ke cikin barayin shanun da suka addabi Anka.

“An kammala binciken farko a kan masu laifin kuma ba da jimawa ba rundunar za ta tura su zuwa hukumomin da ya kamata domin ci gaba da bincike,” in ji Garba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’in WHO na uku da wasu mutane 2 sun kamu da COVID-19 a Bauchi

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta halaka gagararrun 'yan bindiga biyu tare da damke wasu mutum 10 da ake zargi da garkuwa da mutane a kananan hukumomi biyar na jihar.

Kafin haduwar 'yan ta'addan da ajalinsu a ranar Alhamis, an tabbatar da cewa sune ke gallabar jama'ar kananan hukumomin Batsari, Faskari, Charanchi, Dutsinma tare da birnin Katsina.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya sanar da manema labarai cewa an samu bindiga kirar AK 47 guda daya.

Akwai harsasai charbi biyar, babur kirar Bajaj daya, layu da kuma tsabar kudi har N6,465 a tare da 'yan bindigar da aka kashe.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, sun damke wani mutum mai suna Sa'ad Yahaya wanda ya kai wa mahaifinsa farmaki yayin da yake bacci.

Ya yi wa mahaifin fashin N435,000 a yayin da yake bacci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel