Gwamnatin Ganduje ta maidawa Jigawa da Katsina yaran da ke Almajiranci a Jihar Kano

Gwamnatin Ganduje ta maidawa Jigawa da Katsina yaran da ke Almajiranci a Jihar Kano

Bayan bullar cutar COVID-19 a Najeriya, wasu gwamnonin kasar sun fara yunkurin dauke kananan yaran da ke karatun almajiranci da nufin a maida su jihohin asalin da su ka fito.

Gwamnatin Kano ta na cikin wanda ta soma dauke Almajiran da ke jihar. A jiya Laraba mu ka samu labarin cewa an tattara Almajirai har 524 daga Kano, inda aka maida su jihar jigawa.

Gwamnan Jigawa watau Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ne ya karbi wadannan Yara ‘yan ainihin jiharsa. Gwamnati za ta duba lafiyarsu tukuna kafin a ba su damar komawa gidajensu.

Muhammad Badaru Abubakar ya karbi wadannan yara ne da su ka fito daga Kano a sansanin da ake ajiye masu yi wa kasa hidima na NYSC. Gwamnati ce za ta dauki dawainiyar Almajiran.

Kamar yadda wani hadimin gwamnan na Jigawa, Auwal D Sankara, ya shaida a shafinsa na Facebook, gwamnatin jihar za ta kula da abinci da wurin kwannan wadannan masu karatu.

KU KARANTA: Ganduje ya hana wata motar da ta fito daga Madalla shiga Kano

Gwamnatin Ganduje ta maidawa Jigawa da Katsina yaran da ke Almajiranci a Jihar Kano

An maida wasu Almajirai 524 daga Kano zuwa Jihar Jigawa
Source: Instagram

Ba za a kyale Almajiran su shiga gari ba har sai lokacin da aka tabbatar da cewa ba su dauke da wata cuta a jikinsu. Kwamishinan ilmin jihar Kano, Sunusi Kiru ya bayyana wannan a jiya.

Kiru ne ya jagoranci tawagar da ta dawo da wannan yara, ya ce an yi masu gwajin lafiya kafin a fito da su daga Kano. Kawo yanzu dai an samu mutum guda da ya kamu da COVID-19 a Jigawa.

Gwamnatin Jigawa ta ce ba ta da niyyar yin irin abin da makwabaciyarta Kano ta yi na dauke Almajiran da ke karatu a jihar. A cewarta hakan zai yi sanadiyyar kara yada Coronavirus.

Haka zalika gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tattara Almajirai akalla 419 da ke Kano ya maida su jihar Katsina inda su ka fito. Sakataren gwamnatin Katsina ya tabbatar da wannan.

Da ya ke magana da ‘yan jarida, sakataren yada labarai na gwamnatin Katsina, Alhaji Abdullahi Yar’adua ya yi kira ga Iyaye su daina tura yaransu karatu zuwa wuraren da ba su sani ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel