Nwajiuba: Gwamnati ta dakatar da WAEC da NECO saboda annobar cutar COVID-19
Ganin irin barnar da annobar cutar COVID-19 ta ke yi a Duniya, gwamnatin tarayya ta dauki mataki game da jarrabawowin zuwa makarantun gaba da sakandare watau SSCE.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta dakatar da jarrabawar SSCE na wannan shekara har sai nan gaba. Gwamnatin ba ta tsaida wani takamaimen lokaci da za a yi jarrabawar ba.
Minista Emeka Nwajiuba ya sanar da wannan a lokacin da ya ke magana game da matakan da gwamnati ta dauka game da sha’anin ilmi a lokacin wannan annoba ta Coronavirus.
Karamin ministan harkar ilmi na Najeriya ya ce gwamnati ta na kokarin fito da tsari ta yadda ‘yan makaranta za su rika karatu ta kafafen yanar gizo domin su shirya jarrabawar nan gaba.
Jaridar The Cable ta rahoto Emeka Nwajiuba ya na cewa: “An dakatar da jarrabawowin WAEC da NECO har sai baba-ta-gani. ‘Dalibai za su iya yin karatu ta kafafen zamanin yanar gizo.”
KU KARANTA: Za a koyawa yaran makarantu karatu ta gidajen rediyo da talabijin
Nwajiuba ya ce: “Mun yi tanadi sosai a kan yadda ‘yan makaranta za su yi karatu ta yanar gizo. Darektan babban birnin tarayya ya bude dandali na musamman domin wannan tsari.”
“Mu na aiki da ma’aikatar labarai domin yada kayan karatu ga duk wanda ya ke zaune a gida. Kalubalenmu shi ne riskar wadanda ba su da na’ura. Amma mu na aiki da gidajen rediyo.”
Honarabul Nwajiuba ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta kawo wannan shiri a gidajen rediyo domin ‘daliban makarantun firamare da sauran na sakandare.
Kwanakin baya kun ji cewa ana shirya yadda za a rika ilmantar da ‘yan makaranta da ke zaune a gidajensu. Gwamnatin tarayya za ta yi amfani ne da tashoshin rediyo da talabijin na kasa.
A sakamakon shigowar cutar COVID-19, gwamnatin tarayya ta bada umarnin a rufe duk wasu makarantu a watan Maris. Yanzu haka daukacin ‘daliban da ke karatu a Najeriya su na gida.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng