COVID-19: Mun killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar a Otal — Ganduje

COVID-19: Mun killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar a Otal — Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Talata ya ce jihar ta killace wasu mutane da ake zargin suna dauke da kwayar cutar coronavirus a otal domin kare yaduwar cutar a garin.

Premium Times ta ruwaito Ganduje ya ce halin da aka shiga ne ya janyo hakan yayin da ya ke jawabi ga shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu yayin ziyarar da ya kai Kano, Kakakin gwamnan Abba Anwar ya laburta.

Mr Anwar ya ruwaito gwamnan da cewa, "Muna iya kokarin mu domin magance matsalar. Hakan mutane marasa karfi wadanda ake zargin suna dauke da shi ake kai su otal bayan an musu gwaji."

Ganduje ya ce dukkan wadanda aka fara gano wa suna dauke da cutar suna cikin manyan kananan hukumomi da ke cikin gari ne saboda haka an takaita yiwuwar yaduwar ta zuwa wasu unguwanni.

COVID-19: Mun killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar a otal — Ganduje
COVID-19: Mun killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar a otal — Ganduje
Asali: Twitter

DUBA WANNAN An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari

Gwamna Ganduje ya roki NCDC cewa "Akwai bukatar mu kara samar da kayayyakin gwaje-gwaje. Kazalika muna bukatar karin cibiyoyin karbar mutane domin yi musu gwaji."

Kawo yanzu, gwamnan ya ce jihar ba su da wadanda cutar ta yi wa illa sosai ta yadda za su bukaci naurar numfashi ta ventilator da monitor.

Ganduje ya ce yanayin cinkoso da yawan mutanen da ke birnin Kano yana daya daga cikin dalilan da yasa ake samun karuwar wadanda suka kamu da cutar a jihar.

Gwamna ya ce ba abin mamaki bane ganin ana samun karuwar masu cutar. Hakan ya yi kama da abinda ke faruwa a wasu manyan birane na duniya saboda yanayin yawan mutane da ke biranen.

A jawabinsa, shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu ya yabawa kokarin gwamnatin Kano bisa matakan da ta dauka domin yaki da annobar ta coronavirus a jihar.

Shugaban na NCDC ya ce kwamitin kar ta kwana na Kano na cikin mafi kyau a kasar.

Ya fadawa gwamnan cewa, "Muna godiya bisa gudunmawar da ka bawa kwamitin kar ta kwana na jihar. Ba mu da wata zabi illa mu mara maka baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel