Gwamnati ta rufe asibitin da Abba Kyari ya mutu a Legas
Marasa lafiyar da ke ziyartar wasu asibitoci ma su zaman kansu a jihar Legas sun samu sakonnin bukatar su killace kansu saboda su na cikin hatsarin kamuwa da kwayar cutar covid-19.
Asibitocin da yanzu gwamnatin jihar ta rufesu sune kamar haka; St Nicholas, reshen Lagos Island branch; First Cardiology Consultants Hospital da ke Ikoyi, inda Abba Kyari ya mutu, da St Edwards Hospital da ke Ajah.
Sauran sune; Vedic Lifecare Hospital da ke Lekki; County Hospital, Ogba da Premier Specialist Hospital da ke Victoria Island.
A cikin wani sako daban da asibitocin su ka aika wa ma'aikatansu da ma su mu'amala da su a 'yan kwanakin baya bayan nan, sun shawarcesu da su killace kansu, sannan su tuntubi NCDC.
A cikin wata wasika da babban darektan asibitin St Nicholas, Dakta Ebum Bamgboye, ya fitar ranar Litinin, ya ce asibitinsu ya dakatar da aiki na tsawon sati biyu.
Asibitocin sun sallami marasa lafiya a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, yayin da dokar rufe asibitocin na tsawon sati biyu ta fara aiki daga ranar Lahadi, 19 ga wata.
A ranar 18 ga wata ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Farfesa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya a jihar Legas, ya ce marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya mutu ne a wani asibitin kwararru a kan matsalolin zuciya.
DUBA WANNAN: Babbar magana: Gwamnatin Legas za ta gurfanar da wasu ma su cutar covid-19
A wata ganawa da ya taba yi da manema labarai a baya, kwamishinan ya bayyana cewa bashi da masaniyar inda aka kai marigayin yayin da ya dawo Legas bayan an tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.
A cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a shafinsa na Tuwita domin amsa tambayoyi a kan mutuwar Kyari, Farfesa Abayomi ya ce asibitin da aka kwantar da Kyari ya samu sahalewar hukuma domin duba ma su cutar covid-19
A ranar juma'ar makon jiya ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani asibiti mai zaman kansa da aka bawa lasisi ko izinin duba ma su fama da cutar covid-19.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng