Har ila yau: 'Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun sace wasu ma su yawa a Katsina

Har ila yau: 'Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun sace wasu ma su yawa a Katsina

Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun kashe mutane uku tare da raunata wasu mutanen biyu a sabon harin da su ka kai kauyen Sabon Layin Galadima a karamar hukumar Faskari.

Wannan sabon harin na zuwa ne bayan kwana daya kacal da kai wani hari da aka kashe mutane 47 a kauyukan Danmusa da Safana na jihar Katsina.

A ranar Litinin ne mazauna kauyen Sabon Layin galadima su ka shaidawa jaridar 'Daily Trust' cewa 'yan bindigar sun dira kauyen da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi.

A cewarsu, 'yan bindigar, wadanda su ka shiga kauyen a kan babura, sun shafe fiye da sa'a guda su na cin karensu babu babbaka.

"Sun yi awon gaba da dabbobi ma su yawa tare da kone gidajen jama'a," a cewar wani mazaunin kauyen.

Wani mazaunin kauyen ya sanar da Daily Trust cewa, "daga cikin mutanen da suka kashe akwai wani ma'aikacin lafiya mai suna Sanusi Bello, wanda ya zo garinmu daga kauyen Unguwar Doka. Sauran mutane biyun da su ka kashe sune; Safiyanu Abdullahi da Hassan Sani."

Har ila yau: 'Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun sace wasu ma su yawa a Katsina

Gwamnan jihar Katsina; Aminu Masari
Source: Depositphotos

"Sun raunata Ibrahim Hassan da Adamu Ibrahim, wadanda ake cigaba da duba lafiyarsu yanzu haka."

Majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta, ta shaidawa Daily Trust cewa an sake harbe wani mutum tare da sace mutane da dama yayin da su ka fita bayan gari domin neman itacen girki da safiyar ranar Litinin a kauyen Unguwar Doka.

"Sun sace mutane fiye da 40 daga Dandume, Faskari, Funtuwa da Maigora," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: 'Yan arewa 9 da ake kyautata zaton daga cikinsu Buhari zai zabi madadin Abba Kyari

Daily Trust ta ce kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai amsa sakon neman jin ta bakin rundunar 'yan sanda da ta aika masa ba.

Kimanin kwanaki takwas kenan da wasu 'yan bindiga su ka kashe mutum biyu a wasu hare-hare da su ka kai daban - daban a kauyen Sabon Layin Galadima.

Daga cikin mutanen da aka kashe akwai wani manomi mai suna Buhari Umaru, da kuma wani karamin yaro.

Mazauna kauyukan yankin sun bayyana damuwarsu a kan yadda 'yan bindigar ke yawan kai musu hare - hare tare da sace musu baburan hawa da sauran kayan amfani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel