‘Dalibai za su koma karbar karatu ta NTA da FRCN Inji Adamu Adamu

‘Dalibai za su koma karbar karatu ta NTA da FRCN Inji Adamu Adamu

Babban ministan ilmin Najeriya, Adamu Adamu ya bayyana kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi game da ‘daliban makarantun gaba da sakandare da su ke zaune a gida yanzu.

Annobar cutar COVID-19 ta sa an rufe makarantun kasar kwanakin baya. Malam Adamu Adamu ya ce duk da haka ‘daliban makarantun za su rika samun darasi daga cikin gidajensu.

Ministan ilmin ya bayyana cewa za a yi amfani da tashoshin gwamnati na FRCN da NTA wajen shirya darasun ‘yan makarantar. Ministan ya bayyana wannan ne a cikin makon nan.

Da ya ke magana a jiya ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2020, Adamu Adamu ya ce tun kafin barkewar annobar, ma’aikatar ilmi ta fara kokarin kawo wannan tsari a Najeriya.

“Ma’aikatar ta dade da fara tsara wannan, tun kafin ma cutar COVID-19 ta barke, sai dai yanzu ne kawai mutane su ka samu damar samun masaniya kan tsarin.” Inji Malam Adamu.

KU KARANTA:

‘Dalibai za su koma karbar karatu ta NTA da FRCN Inji Minista Adamu Adamu
Yaran Makaranta za su rika koyon karatu ta talabijin gwamnati
Asali: UGC

Ministan ya kuma ce: “Wasu daga cikin makarantunmu na gaba da sakandare sun riga sun fara gudanar da darusa a yanzu, wasu kan gudanar da darasu ne ta kafafen yanar gizo.”

“Ma’aikatar ilmi ta na aiki da gidan talabijin na NTA da gidan rediyon FRCN domin su fara bada darusa, ba wai kawai don annobar COVID-19 ba, ina sa ran wannan shiri ya dore.”

“Saboda haka za a rika bada darasi ta yanar gizo. A lokacin da na gana da shugabannin Jami’o’i, sai da na yi magana da ‘yan jarida, na fada masu su fara shirya darusa a inda su ke.”

“Ina kuma sane da cewa akwai wasu jami’o’in kudi da tuni sun riga sun fara bada darasi ta yanar gizo.” Ministan ya yi wannan jawabi ne a madadin kwamitin yaki da COVID-19.

Sai dai a halin yanzu Malaman jami’a da ke karkashin kungiyar ASUU su na yajin aiki. Tun kafin a rufe makarantu dai gwamnati ta daina biyan wasu daga cikin ma’aikatan albashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel