Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri

Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taya jama’an garin Chibok alhinin cika shekaru 6 tun bayan da mayakan Boko Haram suka sace yan matan.

Wannan tasa gwamnan ya tura wata tawaga domin wakiltarsa wajen jajanta ma iyayen yan matan da yan uwansu, tare da taya su alhinin rashi, sa’annan kuma ya basu sako su kai musu.

KU KARANTA: Baki shi ke yanka wuya: Rubutu a Facebook ya jefa wani mutumi gidan yari

Tawagar ta hada da kwamishinonin ilimi, harkokin mata, rage talauci da mai wakiltar Chibok a majalisar dokokin jahar Borno, kuma sun isar da sakon gwamnan ya iyayen yan matan.

Haka zalika sun mika musu tallafin buhunan shinkafa 500, galolin man gyada 250 da kudi naira miliyan 5.6 don a raba ma iyayen yan mata 112 da har yanzu suke hannun Boko Haram.

Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri
Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri
Asali: Facebook

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne Boko Haram ta kai hari makarantar mata na Chibok inda ta sace dalibai 219, daga bisani gwamnatin Buhari ta kubutar da yanmata 107, ya rage saura 112.

A cikin 107 da suka saki, sun fara ne da guda 1 a watan Mayun 2016, 21 a watan Oktoban 2016, sai guda 82 a watan Janairun 2017, daga nan basu kara sakin kowa ba.

A jawabinsa, kwamishinan ilimi, Bello Ayuba ya bayyana ma iyayen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Zulum ba zasu taba ja da baya ba wajen ceto yayansu.

“Gwamna Zulum ya umarce mu da mu fada muku a duk ganawar da ya yi da shugaban kasa Buhari, Buharin yana nuna damuwarsa da halin da kuke ciki, tare da alkawarin tabbatar da ya ceto yaranku.

“Shugaban kasa da Gwamna suna da yara mata, babu wasu iyayen kirki da zasu hakura da neman yaransu da suka bata, suna ta kokari, kuma da ikon Allah zasu ceto su da ransu.” Inji shi.

Da su ke godiya ta bakin wakilinsu Yakubu Keke, iyayen yan matan sun bayyana farin cikinsu ga tallafin da gwamnan ya basu, kuma sun ji dadin yadda yake nuna damuwa a kansu.

Daga karshe Yakubu Keke ya yi kira ga gwamnan da ya cigaba da tuna ma shugaban kasa halin da suke ciki har sai an ceto yan matan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel