Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cafke wata mata mai suna Fatima Garba da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da suka addabi jama'ar jihohin Sokoto, Kebbi, Kaduna da Neja.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya na kasa, Frank Mba, ya fitar a ranar Talata, ya ce Fatima ta na safara tare da boyewa 'yan ta'addar makamansu.
Fatima, wacce ta amsa laifinta da bakinta, ta bayyana cewa 'yan ta'addar na ba ta kudi masu tsoka duk lokacin da suka dawo da makamansu bayan sun fita aiki.
Ta bayyana cewa ta na boye makaman ne a cikin wani rami a gidanta, sannan ta ce ta san laifi ake aikatawa dasu.
Binciken rundunar 'yan sanda ya gano cewa Fatima ta shiga wannan muguwar sana'a ne ta hannun wani saurayinta mai suna Abubakar Usman.
Sauran 'yan tawagar kungiyar 'yan ta'addar da aka kama tare da Fatima sun hada da; Sama'ila Usman, mai shekaru 28, Mohammed Ibrahim, mai shekaru 30, Mohammed Agali, mai shekaru 22 da Shamsu Mohammed, mai shekaru 30.
Sauran sun hada da; Mohammed Usman, mai shekaru 37, Umar Abdullahi, mai shekaru 33, Buhari Abubakar, mai shekaru 33, da Abubakar Garba, mai shekaru 37.
An yi kiyasin cewa tawagar 'yan ta'addar sun samu kudi fiye da miliyan goma sha biyu daga aiyukan ta'addanci daban-daban da suka aikata.
DUBA WANNAN: FG ta gimtse shirin bayar da tallafin N20,000 a jihohi hudu
Makaman da aka kama tare da 'yan ta'addar sun hada da; bindiga samfurin AK47 guda biyar, babbar bindiga samfurin G3 guda daya, da wata karamar bindiga (Beretta pistol) guda daya.
Sauran makaman sun hada da alburusai carbi 1476, carbi 36 na bindigar G3, kwanson aburushin AK47 guda 6, motar hawa guda daya, wayar salula guda 8, da wata akwati mai dauke da kayan aiki daban-daban.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng