Dalilin da ya sa ban hana zirga-zirga a Jihar Kuros-Riba ba – Inji Ben Ayade
Domin hana yaduwar cutar COVID-19, wasu gwamnoni da-dama sun rufe iyakokinsu, har ta kai a wasu jihohin gwamnati ta maka takunkumin haramta fita na tsawon makonni.
Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros-Riba ya bayyana abin da ya sa bai bada umarni a rufe Gari gaba daya ba kamar yadda ake yi a wasu Kasashen ketare da ma jihohin Najeriya.
Ben Ayade ya na ganin cewa kare rayukan jama’a ba tare da kare hanyar samun abincinsu ba zai iya jefa kasar cikin wata sabuwar matsala dabam bayan annobar cutar Coronavirus.
“Wasu ‘Yanuwanmu Maza da Mata sun dogara ne da fita kwadago kullum domin su samu abinci. Idan ka na daukar kankare ne a duk ranar Duniya, a ranar da aka hana ka zuwa aiki, ba za ka samu kudin da za ka ciyar da ‘Ya ‘yanka ba.” Inji Mai girma Gwamna Ayade.
A dalilin haka, gwamnan ya ce ya na adawa da rufe jihar, ya ce gara a kyale mutane su cigaba da harkokin gabansu su nemi kudi muddin sun rufe fuskarsu da tsummar kariya.
KU KARANTA: Masu dauke da cutar Coronovirus sun kai mutum 343 - NCDC
Ayade ya yi wani karin bayani: “A fadin Duniya, yunuwa da makamantan cututtukanta irinsu Kwashiorkor da Tarin TB su kan kashe mutane kusan miliyan 8.4 a duk shekara.”
Don haka ne gwamnan ya ke ganin cewa babu wata annoba da ta fi yunwa a Duniya. “Za mu yi duk abin da za mu iya na takaita yaduwar wannan annoba a cikin jiharmu.”
“Za kuma mu kare rayukan Jama’a, amma kuma akwai tangarda wajen kare rai ba tare da an tsare hanyar da za ta samu abinci ba. Dole a samu kyakkyawar alaka tsakaninsu.”
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne ga Manema labarai a Ranar Litinin a Garin Kalaba. Gwamna Ayade ya fi maida hankali ga amfani da tsummar rufe fuska.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng