Biyu sun mutu, 17 su na kwance asibiti bayan cin abinci mai guba a gidan biki a Katsina

Biyu sun mutu, 17 su na kwance asibiti bayan cin abinci mai guba a gidan biki a Katsina

Mutane biyu sun mutu yayin da wasu 17 suna kwance a asibiti bayan sun ci abincin da ake zargin akwai guba a cikinsa a wurin biki a Katsina.

Mutane biyu da suka mutu, Bilkisu Surajo mai shekaru 20 da Ibrahim Sani mai shekaru 13 duk yan kasar jamhuriyar Nijar ne da ke makwabtaka da Katsina.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya ce tuni an damke wasu mutane biyu da ake zarginsu da saka gubar cikin abincin.

Rahoton da yan sanda suka rubuta ya ce wani matashi mai shekaru 25, Musa Suleiman ne ya hada baki da wata Shafaatu Surajo inda suka saka Zaqami a cikin abincin da za a bawa yan biki.

Katsina: Mutum 2 sun mutu, 17 suna kwance asibiti bayan cin abincin gidan biki
Katsina: Mutum 2 sun mutu, 17 suna kwance asibiti bayan cin abincin gidan biki
Asali: Depositphotos

Dukkansu biyu suna zaune ne a gida daya da ke kauyen Ali Yaba da ke yankin Mani a jihar ta Katsina.

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Tuni dai an kama su kuma sun amsa cewa sun saka Zaqamin cikin abincin bikin.

Wani takaitacen bidiyon da yan sanda suka fitar ya nuna Shafaatu tana amsa cewa Musa ya bata shinkafa da ruwa a bokiti domin ta dafa abincin da baki za su ci.

Musa shima ya amsa cewa ya bata kayayyakin amma bai bayyana dalilin da yasa ya ba ta ba.

Kazalika, a ranar 7 da 9 na watan Afrilun 2020 tsakanin karfe 12 na dare da 5 na asubahi, Yan sandan operation uff adder sun dakile wata hari da barayin shanu suka kai kauyukan Dan Alhaji da Zamfarawa.

Sun kama wani Abubakar Maiunguwa Alti mai shekaru 26 da ke zaune a rugar Fulani na Dogon Dutsen Akata a garin Batsari na jihar Katsina inda suka kwato shanu a hannunsa.

Alti ya yi kaurin suna wurin taaddanci kuma ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka kai hare-hare a kauyukan Batsari duk dai a jihar ta Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel